Masu son Birtaniya ta fita daga Tarayyar Turai ’yan wuta ne – Shugaban EU

Shugaban Kungiyar Tarrayar Turai, Donald Tusk ya bayyana wadanda suke so Birtaniya ta fice daga Tarrayar Turai ba tare da wani kyakkyawan shiri ba a matsayin “’yan wuta.’’ Ya bayyana haka ne bayan tattaunawarsu da Ministan Ireland Leo Baradkar a Brussels. Ya ce Tarrayar Turai za ta matsa lamba a kan yarjejeniyar barin iyakar kasar […]

Masu son Birtaniya ta fita daga Tarayyar Turai ’yan wuta ne – Shugaban EU

Shugaban Kungiyar Tarrayar Turai, Donald Tusk ya bayyana wadanda suke so Birtaniya ta fice daga Tarrayar Turai ba tare da wani kyakkyawan shiri ba a matsayin “’yan wuta.’’

Ya bayyana haka ne bayan tattaunawarsu da Ministan Ireland Leo Baradkar a Brussels.

Ya ce Tarrayar Turai za ta matsa lamba a kan yarjejeniyar barin iyakar kasar Ireland a bude ko da kuwa akwai batun ficewar Birtaniya domin a samu zaman lafiya.

Amma Mista Tusk da kuma Mista Baradkhar suna da shirin ko-ta-kwana a kan batun ficewar Birtaniya daga Tarrayar Turan.

’Yan Majalisar Dokokin Birtaniya irin su Andrea Leadsom tuni suka fara mayar da martani a kan wadannan kalamai na Mista Tusk.

Misis Leadsom, wadda tana daya daga cikin wadanda suka yi ta kiraye-kirayen ficewar Birtaniya, ta bayyana kalaman a matsayin “kalaman da-na-sani’’ kuma ‘“kalaman da ba za su taimaka ba.’’

’Yar majalisar, wadda kuma ’yar Jami’iyyar Conserbatibe ce ta shaida wa BBC cewa Tusk “ba ya da da’a.’’

A kwanakin baya ne ’yan Majalisar Dokoin Birtaniya suka fitar da wasu sababbin shawarwari domin sauya makomar kasar a kan batun ficewarta daga Tarayyar Turai da ake kira Bredit.