Masu son kai ne suka fice daga APC – Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa dukan wadanda suka fice daga Jam’iyyar APC zuwa sauran jam’iyyu mutane ne masu son kansu kuma ragwaye, wadanda ba za su iya tafiya a bisa turbar muradin  wannan gwamnati mai ci a yanzu ta sa a gaba ba. Shugaba Buhari ya yi wannan jawabi ne a ranar Talatar […]

Masu son kai ne suka fice daga APC – Buhari
Masu son kai ne suka fice daga APC – Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa dukan wadanda suka fice daga Jam’iyyar APC zuwa sauran jam’iyyu mutane ne masu son kansu kuma ragwaye, wadanda ba za su iya tafiya a bisa turbar muradin  wannan gwamnati mai ci a yanzu ta sa a gaba ba.

Shugaba Buhari ya yi wannan jawabi ne a ranar Talatar da ta gabata, lokacin da yake karbar fom na neman tsayawa takarar Shugaban kasa a zaben 2019 karkashin Jam’iyyar APC da wata kungiya mai suna ‘Nigerian Consolidation Ambassadors Network (NCAN) ta saya masa.

Wadannan kalamai na Shugaban kasa dai  martani ne ga wadansu jiga-jigan jam’iyyar da suka fice a watan Yuli da suka hada da Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki da gwamnonin jihohin Sakkwato da Neja da Benuwai da wasu sanatoci da ’yan Majalisar  Wakilai da dama.

Buhari ya nanata cewa a yanzu cin hanci da rashawa da aka fara murna an kusa murkushe shi, sai ga shi ya juyo a guje yana yakar kasar nan. “Amma yanzu muna da jam’iyya mai cike da nagartattun mutanen da ke da muradin yi wa al’umma aiki tukuru, domin tabbatar da samun kasaitacciyar Najeriya,” inji shi.0

Sai ya nuna godiyarsa tare da jinjina ga kungiyar da ta saya masa fom din a kan Naira miliyan 50. Yana mai cewa muradinsa na ceto Najeriya ya fara ne tun daga shekarar 2002. “Najeriya ta kusa fadawa ramin da ba ta iya fitowa a cikin shekarar 2006, inda wadansu mutane masu mummunar manufa suka wulakantar da zaben 2007,”  inji shi.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa