Masu son Sarki Ado ya mutu ne suka raba ni da mukamin Wazirin Kano – Sheikh Nasir

Sheikh Nasir Muhammad Nasir, Limamin Masallacin Juma’a na Waje ko Fagge da ke Kano, wanda marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero ya nada Wazirin Kano, amma gwamnatin Jihar Kano ta soke nadin nasa, ya bayyana wa wakilanmu alakarsa da marigayi Sarki Ado kuma, a cewarsa, har sarki ya rasu shi ne a matsayin Waziri a […]

Masu son Sarki Ado ya mutu ne suka raba ni da mukamin Wazirin Kano – Sheikh Nasir
Masu son Sarki Ado ya mutu ne suka raba ni da mukamin Wazirin Kano – Sheikh Nasir

Sheikh Nasir Muhammad Nasir, Limamin Masallacin Juma’a na Waje ko Fagge da ke Kano, wanda marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero ya nada Wazirin Kano, amma gwamnatin Jihar Kano ta soke nadin nasa, ya bayyana wa wakilanmu alakarsa da marigayi Sarki Ado kuma, a cewarsa, har sarki ya rasu shi ne a matsayin Waziri a wajensa. Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Me za ka ce game da halin da ake ciki bayan rasuwar Sarkin Kano, Alhaji Dokta Ado Bayero, wanda kowa ya san amininka ne kuma bayan rasuwarsa Ubangiji Ya sa an samu wanda ya gaje shi har an nada sabon Sarki?
Sheikh Nasir: Bismillahir Rahmanir Rahim, Wa sallallahu Ala Nabiyyil Karim. To da farko dai muna godiya ga Allah Madaukakin Sarki, Mai kowa, Mai komai. Muna kara salati da sallamawa ga Annabi Muhammadu, Sallallahu Alaihi Wa Sallama. Ina ta’aziyya ga daukacin jama’ar Kano da masoyan mai martaba sarki na jihohi daban-daban a fadin Najeriya da ma na kasashen wajen a bisa hakurin wannan gagarumin rashi nasa da muka yi. Ubangiji Ya jikansa, Ya rahamshe shi, kuma Ya sada  shi da Manzon Allah (SAW).
Kamar dai yadda Ubangiji Ya ce da Ma’aikin Allah ne cewa, tun da shi ma zai rasu, to kuwa babu wanda zai dawwama a duniyar nan, sai ya mutu. Haka nan bayani ya zo cewa wanda duk ya rasu, to Alkiyamarsa ta tsaya.
Muna kuma godiya ga Ubangiji da Ya kaddara, Ya bai wa dan dan uwan Ado Bayero sarki a bayansa, kuma muna kira ga jama’a da su yi biyayya ga sabon Sarki Sanusi Lamido, saboda wannan nufi ne na Allah kuma Allah Yana aikata duk yadda Ya so, ba tare da Ya shawarci kowa ba. Ina kuma gargadin jama’a da kada su saurari makiya da mahassada, kamar yadda ta faru a kanmu a lokacin da mai martaba sarki ya nada mu a matsayin Wazirin Kano.
Wadansu mutane sun fito fili sun nuna kiyayyarsu da bakin cikinsu da matsayin da aka ba mu, sai dai kuma Allah Ya fi su har wannan abu ya tabbata. Ubangiji Ya nufi masoyinmu sarki da nada mu Waziri a ranar Juma’a 30 ga watan Mayu, kuma ya yi ne don nuna mini kauna, kuma ni a nan sarki ya gama yi mini komai, babu abin da zan ce da shi, sai godiya. Amma makiya kuma mahassada suka tashi a tsaye, sai da suka ga an raba ni da mukamin.
Wadannan mutane sun ci amanar sarki, sun kuma ci amanar ’ya’yansa, sannan sun ci amanar gwamnan Kano, domin sun rude shi ne, amma shi ya yi abin da ya yi ne a bisa kyakkyawar niyya. Ni ko kadan ba na ganin laifin Mai girma gwamna, domin babu kiyayya a tsakanina da shi. Idan da a ce akwai kiyayya da bai zo wajenmu ba a lokacin yana neman takarar zama gwaman. Kuma ba sau daya ba, ba sau biyu ba, a gaban tarin mabiyansa, ya roki mu yi masa addu’a kuma muka yi masa.
Duk wannan abu makiya sarki ne da suka damu da ya rasu don suna kwadayin za su samu mulki, amma Ubangiji bai kawo rasuwarsa ba. A cikinsu ne aka samu wani ya yaudari sarki, ya ci amanarsa. Shi ne da suka ga wannan makircin nasu bai kai ga karya zuciyar sarki ko rasuwarsa ba, sai suka sake bullowa da wani makircin da zai tayar wa sarki hankali, sai suka shiga Rediyo suka bayar da sanarwa cewa masarauta ta janye nadin da sarki ya yi mini, amma sun yi hakan ne ba da yawunsa ba.
Amma kuma a wajena wannan aikin jahilci ne, domin yaya wani zai ba ka riga, sannan wani daban ya ce zai zo ya cire ta daga wuyanka? Sannan me ya sa za su yi haka idan da ma ba sun damu da sai sarki ya rasu ba?  Ina da tabbacin ba don ajalin sarki ya yi ba da sai ya tube su daga mukamansu. Kuma sarki ya rasu ne daga bugun zuciyar da ya samu.
Don haka ni da duk mabiyana, ba mu da wani kulli tsakaninmu da sabon sarki. Muna yi masa fatar alheri kuma ba mu da wata gaba tsakaninmu da shi. Game da hassada kuwa, a kullum ina rokon mahassadana su karu su yi yawa, domin yawan mahassadan mutum yana nuna girman darajarsa, kuma duk ma’abocin ni’ima shi ake yi wa hassada.
Kamar yadda wata mace daga Banu-Isra’ila ta je gaban Annabi (SAW) tana yi masa addu’ar cewa Allah Ya kara masa yawan masassada, sai Sayyadina Umar ya fusata, amma Annabi ya ce a tambaye ta dalilin yin hakan, sai ta ce saboda a addininsu an fada musu cewa mafifitan mutane su ne wadanda ake yi musu hassada. Don haka a kullum nake bayyana addu’ata cewa, “Allah Ya kara mini yawan mahassada.”
Aminiya: Duk da cewa tsakaninka da marigayi Ado Bayero ba boyayyen abu ba ne, amma wadansu za su so su ji irin yadda matsayin alakarku take da yadda ta fara.
Sheikh Nasir: Sheikh Nasir yin wannan tambayar kamar mutum ne ya ce zai tambayi mece ce alakar Manzon Allah (SAW) ne a tsakaninsa da babban sahabinsa, Sayyadina Abubakar (RA). Domin kuwa haduwata da mai martaba Ado Bayero akalla ta fi shekara 30 muna tare, kuma mun yi tafiye-tafiye har mun je aikin Hajji wajen Manzon Allah, (SAW) ya fi sau dari.
Haka nan wannan soyayyar tawa da sarkin ce ma ta sanya ya nada ni matsayin Wazirin Kano a ranar 30 ga watan Mayu wanda ya gabata, amma kuma sai wadansu makiya, mahassada, masu bakar aniya kuma maciya amana suka yi kulle-kulle har suka rudi gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso ya amince da a sauke ni. Sai dai ni ko kadan ba na ganin laifin gwamna Kwankwaso a cikin maganar don na tabbatar an shirya masa munafunci ne ya hau kai ba tare da ya fahimta ba.
Don haka duk wadannan maganganu da ake yi, ni ba mai yawan yin magana ba ne, kuma ba dan siyasa ba ne. Da harkar karatu ce sai na yi ta yi zuwa lokaci mai yawa ba tare da damuwa ba. Amma dai wadannan makiyan su ne suka sako ni a gaba suke son ganin karshena.
Kuma wadanda suka shirya wannan makircin kamar mutanen gidan shawara ne na Darun Nadwah da suka taru suke shawarar yadda za su halaka Annabi (SAW). Kuma idan Allah Ya so sai makircinsu ya bi su, don Allah ba azzalumin Sarki ba ne. Na mika lamarina ga Allah.
Aminiya: Yaya kuma maganar mukaminka na Limancin masallacin Waje? Me ya faru da shi?
Sheikh Nasir: Wannan abu da ya faru na je da kaina na ce na ajiye mukamin sarauta ta Waziri, sannan na ce na sauka daga mukamina na dan majalisar sarki. Amma kuma har yanzu ina rike da mukamina na Limamin Masallacin waje. Domin ko shi ma sarki ne ya nada ni. Ina godiya ga Ubangiji.
Godiyar da nake wa Ubangiji, yadda marigayi sarki ya rike ni da aminci har ya fi duk wani mukami da ya ba ni, har ma na Waziri, domin da zai rasu ya bayar da wasiyya a rubuce cewa ni zan yi masa wanka kuma na sallace shi, kuma kowa ya gani, hakan aka yi. Kuma har sarki ya rasu ni ne matsayin Waziri a wajensa, domin saura kwana 5 da rasuwarsa ya aiko Shamaki cewa ranar Juma’ar da Ubangiji Ya yi masa cikawa, na je fada a nuna min gurbina na zama a fada, sai kuma ta Allah ta kasance a gare shi. Don haka babu abin da zan ce in banda godiyar Allah. Shi kuma sarki muna yi masa addu’a Ubangiji Ya sada shi da Annabi (SAW).