Masu son talauci ne kawai za su zabi Jonathan – Osinbajo
Mataimakin dan takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC Farfesa Yemi Osinbajo ya ce mugun halin da tattalin arzikin kasar nan ya shiga ya jefa ’yan Najeriya da dama cikin kuncin talauci, don haka akwai bukatar a samu canji gwamnati a matakin tarayya domin ceto ‘’yan Najeriya daga kangin talauci.Farfesa Osinbajo wanda tsohon Babban Lauyan […]
Mataimakin dan takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC Farfesa Yemi Osinbajo ya ce mugun halin da tattalin arzikin kasar nan ya shiga ya jefa ’yan Najeriya da dama cikin kuncin talauci, don haka akwai bukatar a samu canji gwamnati a matakin tarayya domin ceto ‘’yan Najeriya daga kangin talauci.
Farfesa Osinbajo wanda tsohon Babban Lauyan Jihar Legas ne ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa da masu sana’o’in hannu da ’yan kasuwa da manoma da gwamnatin Jihar Legas ta shirya a Ikeja a ranar Talata.
Ya ce, wadanda suke son talauci talauci kuma suke son ci gaba da zama da yunwa ne kawai za su zabi Shugaba Goodluck Jonathan a zaben bana.
Osinbajo ya ce “Babu wanda bai san abin da ke faruwa a kasar nan ba. Babu wanda yake son yunwa da talauci, amma mutane suna fama da yunwa. A shekarar 2015, wadanda kawai suke son ci gaba da zama da yunwa ne za su kaunaci gwamnatin da ke kan gado ta ci gaba da mulki. Amma da yardarm Allah za mu cire su daga kujerar mulki. Mutanen da suke mulki a yanzu ba za su iya yin komai ba, saboda ba su san abin da ya kamata su yi ba. Ba su da kwarewa ko cancanta ta gudanar da mulkin kasar nan.”
Shi kuwa dan takarar Gwamnan Jihar Legas a karkaashin Jam’iyyar APC, Mista Akinwunmi Ambode ya ce, APC tun daga zamanin Bola Tinubu zuwa Gwamna Babatunde Fashola ta ci gaba da samar da kyakkyawan shugabanci ga jama’ar jihar, inda ya ce idan aka zabe shi gwamnatinsa ba za ta karkace daga wannan tafarki ba.