Masu sufurin jiragen ruwa sun yi alkawarin tabbatar da nasarar tashoshin Teku-Huta
Manajan Daraktan Kamfanin Sufurin Jiragen Ruwa na CMA CGM Nigeria Limited, Mista Todd Ribers ya bayar da tabbacin cewa tashoshin Teku-Huta da aka bullo da su za su kasance masu alfanu da amfani ga dukan masu ruwa-da-tsaki da suke harkar fiton kayayyaki a kasar nan. Tashoshin Teku-Huta da Hukumar Sufurin Jiragen Ruwa ta Najeriya ta […]

Manajan Daraktan Kamfanin Sufurin Jiragen Ruwa na CMA CGM Nigeria Limited, Mista Todd Ribers ya bayar da tabbacin cewa tashoshin Teku-Huta da aka bullo da su za su kasance masu alfanu da amfani ga dukan masu ruwa-da-tsaki da suke harkar fiton kayayyaki a kasar nan.
Tashoshin Teku-Huta da Hukumar Sufurin Jiragen Ruwa ta Najeriya ta bullo da su, an bullo da su ne domin rage cinkoso a tashoshin jiragen ruwa tare da kusanto da harkokin shigi da ficin kayayyaki kusa da jama’ar da suke tudu.
Riber ya bayar da tabbacin ne a wajen taron masu ruwa-da-tsaki da aka kira domin fadakarwa kan ayyukan tashar Teku-Huta ta Kaduna da aka kaddamar kwanakin baya. Tashar Teku-Huta ta Kaduna tana daga cikin tashoshi irinta bakwai da Gwamnatin Tarayya ta amince da su.
Shugaban na CGM, wanda ya halarci taron, ya ce, mambobinsu suna shirye su hada hannu da dukan hukumomin da suka kamata don cimma nasarar tashoshin.
Ya ce, “Koyaushe muna hada hannu da Hukumar Sufurin Jiragen Ruwa (NSC) da Hukumar Kwastam da Hukumar Kula da Tashoshin Ruwa ta Najeriya, kuma muna shirye mu goya wa tashar Teku-huta ta Kaduna domin wannan shiri ne da zai amfani Najeriya kuma ya amfani tattalin arziki kuma ya amfani harkokin kasuwancinmu.”
Ya kara da cewa, “Najeriya ce babbar kasuwarmu, kuma muna son mu ci gaba da taka rawa a bangarenmu domin bunkasa kasar nan. Kuma bai kamata wannan fadakarwa ta tsaya a nan ba. Mu hada da yin aikin da zai tabbatar da nasarar tashoshin Teku-Huta. Mu ’yan kasuwa ne da muke son samun riba, kuma za mu tallata wannan manufa ga abokan cinikinmu.”
Shugaban Hukumar NSC, Barista Hassan Bello wanda ya jagoranci taron ya shawarci masu gudanar da tashohin jiragen ruwan a kan kada su rika daukar kansu a matsayin abokan gasa da masu gudanar da tashar Teku- Huta. Maimakon haka, ya ce, kamata ya yi su rika kallonsu a matsayin wadanda za su taimaka musu wajen saukake musu aiki.
Barista Bello ya ce Gwamnatin Tarayya tana matukar shaukin ganin an samu nasarar gudanar da tashoshin.
Ya bukaci masu ruwa-da-tsaki su hada kai don saukaka gudanar da ayyukan tashoshin Teku-Hutar, “Dalilin wannan taro shi ne a samu shawarwari da hadin kan masu ruwa-da-tsaki a wannan bangare kan yadda ya kamata a gudanar da tashar. Wannan somin tabi ne, kuma kamar yadda kuka sani ne, duk wani sabon lamari yakan zo da matsaloli. Amma ina ganin idan muka yi aiki tukuru, za mu samu abin da muke so. Ba Hukumar Sufurin Jiragen Ruwa kadai ce ke yin aikin ba. Shekara 10 da suka wuce, an kafa wani kwamitin lura da aiki wanda ya kunshi kusan kowa, ciki har da Hukumar Kwastam da Hukumar Jiragen kasa da masu manyan motocin dakon kaya da masu fito da kuma abin farin ciki kamfanoni sufurin jirgen ruwa da masu gudanar da tashoshin jiragen ruwa wadanda suke da matukar muhimmanci ga nasarar wannan shiri,” inji shi.
Barista Bello ya bukaci masu amfani da tashoshin da kada su damu da matsalolin tantance kaya idan suka fara amfani da tashar Teku-Huta, inda ya ba su tabbacin cewa za a fitar da sababbin tsare-tsare, duk da cewa dole su yi biyayya ga dokokin Hukumar Kwastam na shigo da kaya da fitar da shi.