Masu sukar gwamnatin Buhari munafukai ne – Alhaji Jibrila

Wani dan kasuwa mai hada-hadar canjin kudaden waje, mazaunin garin Benin Jihar Edo, Alhaji jibril Abdallah ya kalubalanci masu fadin cewa ba su ga canji ba a wannan gwamnati mai ci ta Shugaban kasa Muhammadu Buhari da cewa zance ne suke yi mara kan gado. Ya ce irin wadannan mutane da ke wannan magana maciya […]

Masu sukar gwamnatin Buhari munafukai ne – Alhaji Jibrila
Masu sukar gwamnatin Buhari munafukai ne – Alhaji Jibrila

Wani dan kasuwa mai hada-hadar canjin kudaden waje, mazaunin garin Benin Jihar Edo, Alhaji jibril Abdallah ya kalubalanci masu fadin cewa ba su ga canji ba a wannan gwamnati mai ci ta Shugaban kasa Muhammadu Buhari da cewa zance ne suke yi mara kan gado. Ya ce irin wadannan mutane da ke wannan magana maciya amanar kasa ne, ba daidai ba ne a ce an tsaya ana sauraron su, domin nade tabarmar kunya ce hauka da suke yi.
Ya ci gaba da cewa: “Ya kamata masu hankali ’yan Najeriya su auna irin yawan barnar da wadannan azzalumai marasa kishin kasa suka tabka tsawon shekara goma sha shida da suka yi suna cin karensu ba tare da babbaka ba, a cikinsu wane ne ya tuna da ya yi wa talaka aikin alheri? Sai mu dawo mu duba watanni shida da wannan bawan Allah Buhari ya yi a kan kujerar shugabancin kasar nan, wanda ya karbi mulki a cikin wannan mummunan yanayi da barnar da wadannan maciya amanar kasa suka tafka.
“Kuma a cikin wadannan watannin, har ya kawo zaman lafiya ta fara samun karfi da dorewa a kasar nan. Domin kafin karbarsa mulki daga hannun wadannan kurayen, idan muka yi la’akari da abin da ya rika faruwa a yankin Arewa maso gabas a can baya cikin gwamnatin da ta gabata; inda kungiyar Boko Haram suka mamaye suka maida yankin tamkar hanya ce ta zuwa a tafi barzahu.”
dan kasuwar ya karashe bayaninsa da cewa: “Mu dai yanzu abin da muka fahimta ga irin wadannan mutane, sun gama kashe kasar nan. Don haka ba za mu taba mu amince da su ba har Mahdi ya bayyana kuma muna bai wa Gwamnatin Buhari goyon baya dari-bisa-dari, domin irin kwanciyar hankali da muka samu a cikin wannan gwamnatin, muna tafiyar da sana’armu da sauran harkokinmu cikin lumana, babu tashin hankali. Alhamdu lillahi, mun gode Allah.”