Masu tabin hankali sun koka kan rashin tallafin magani daga gwamnati
Masu fama da tabin hankali da suke jinya a Jihar Kebbi sun koka kan rashin samun tallafin magani daga hannun gwamnatin jihar. Sun koka ne kan rashin ba su magani duk mako a asibitin garin Zauro da ke Karamar Hukumar Birnin-Kebbi a karkashin shirin bayar da tallafin magani ga masu tabin hankali da farfadiya da […]
Masu fama da tabin hankali da suke jinya a Jihar Kebbi sun koka kan rashin samun tallafin magani daga hannun gwamnatin jihar. Sun koka ne kan rashin ba su magani duk mako a asibitin garin Zauro da ke Karamar Hukumar Birnin-Kebbi a karkashin shirin bayar da tallafin magani ga masu tabin hankali da farfadiya da hawan jini da sauran marasa lafiya da ba su da hali da aka faro lokacin gwamnatin sojoji a jihar.
Binciken Aminiya ya gano a yanzu bayar da tallafin maganin ga masu tabin hankalin da sauransu da suka fito daga kananan hukumomi 21 na jihar ya samu cikas, inda majinyata ke cikin halin kaka-ni-ka-yi kan rashin magungunan.
Aminiya ta gano majinyata na karuwa a wurin karbar magani na asibitin Hajiya Turai ’Yar’aduwa da ke Zauro, inda wata majiya ta ce akalla likitoci sun tantance mutum 15,280 domin tallafa musu da maganin da za su rika amfani da shi kyauta, sai dai har yanzu babu wani labari kan yiwuwar samun tallafin maganin gare su. Aminiya ta ziyarci asibitin a garin Zauro domin jin ta bakin marasa lafiyar, dakwamitin da ke kula da karbar magani da kuma hukumomin gwamnati da matsalar ta shafa a jihar.
Wani mai ciwon farfadiya mai suna Umar Barti daga Karamar Hukumar Augie ya bayyana wa Aminiya cewa suna zuwa karbar magani kowane mako a asibitin Zauro, kuma tun lokacin gwamntin Adamu Aliero ya fara karbar magani a asibitin har zuwa yau. Kuma ya ce “Yanzu kimanin wata shida ke nan muna zuwa karbar magani a asibiti ana ce mana babu magani sai an kawo. Saboda haka mun gaji da baro garuruwanmu kuma ba mu samun magani. Muna kira ga gwamnatin jiha da hukumomin da abin ya shafa su taimaka wa marasa lafiya da ke karbar magani a asibitin Zauro domin mun kai wata shida rabon mu da magani.”
Shi ma wani mai fama da rashin lafiyar tabin hankali mai suna Malam Bande Aliyu daga Karamar Hukumar Bagudo ya ce watansu shida rabonsu da su samu magani “Bayan mun fara jin dama-dama sai ga shi babu tallafin da ake ba mu na magani. Saboda haka muna rokon gwamnati da wadanda abin ya shafa su taimaka su kawo magani a asibitin domin mu ci gaba da karba,” inji shi. Ya ce yanzu haka likitocin da suke duba su sun bar shigowa asibitin balle idan wata matsala tana damunsu su gaya musu.
Wata mata mai matsalar fitsarin kwance da ta nemi a sakaye sunanta ta ce “Saboda maganin da take karba duk mako matsalar da take fama da ita ta ragu sosai, amma yanzu da ta kai wata bakwai ba ta samu magani ba, matsalar ta dawo har mijinta ya sake ta. “Domin Allah muna kira ga duk wanda ke da alhaki ga kawo magani a asibitin Zauro ya taimaka ko su taimaka,” inji ta.
Ta ce “Farko na fara samun matsalar tabin hankali amma da aka rika ba ni magani a asibitin Zauro kuma aka dauki nauyin kai ni asibitin Kware da ke Jihar Sakkwato sai na samu lafiya har na yi aure. Daga baya sai matsalar fitsarin kwance ta kama ni wanda nake karba magani a kai.” Ta ce “Wannan tallafin bayar da magani ga marasa lafiya irin daban-daban ba karamin taimako ya yi ba. Saboda Allah a taimaka wa marasa lafiya a Jihar Kebbi domin muna cikin halin kaka-ni-ka-yi.”
Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin hukumomin gwamnatin Jihar Kebbi kan wannan matsalar ta rashin bayar da tallafin magani ga masu tabin hankali da sauran marasa lafiya a jihar amma bai samu nasara ba.
A lokacin da wakilinmu ya ziyarci Hukumar Zakka da Sadakoki ta Jihar wadda ita ke bayar da tallafin bai samu ko daya daga cikin shugabannin hukumar ba, don jin abin da ya sa aka dakatar da bayar da tallafin maganin. Haka a asibitin Zauro ma’aikata da shugabannin asibitin sun ki yi tsokaci kan rashin bayar da tallafin maganin ga marasa lafiya.