Masu tattakin domin Obasanjo sun ci kwakwa

Tun  lokacin da matashin nan Sulaiman Hashim ya yi tattaki daga Legas zuwa Abuja domin cika alkawarin da ya ce ya dade da dauka idan har Muhammadu Buhari ya zama shugaban kasa, mutane da yawa hatta mata suma suka ara suka yafa suna tafiya a kasa don ganawa da gwaninsu a wasu jahohi. Mutun hudun […]

Masu tattakin domin Obasanjo sun ci kwakwa
Masu tattakin domin Obasanjo sun ci kwakwa

Tun  lokacin da matashin nan Sulaiman Hashim ya yi tattaki daga Legas zuwa Abuja domin cika alkawarin da ya ce ya dade da dauka idan har Muhammadu Buhari ya zama shugaban kasa, mutane da yawa hatta mata suma suka ara suka yafa suna tafiya a kasa don ganawa da gwaninsu a wasu jahohi.
Mutun hudun da suka zanta da Aminiya saboda burinsu na ganin tsohon shugaban kasa cif Olusegun Obasanjo, sun ce duk wani kokari da suka yi dan su ganshi abin ya ci tura, duk da tafiyar da suka sha a kasa da keke da kuma kwanakin da suka yi a hanya.
Sa’idu Abdullahi, wanda ya bar matar sa da ‘ya’ya tara ya dauko keke tun daga karamar hukumar Chikum a Jahar Kaduna, ya ce ya kwana 10 a hanya kafin ya shiga garin Abeokuta. Ya ce a ranar da ya je garin ya hadu da wata mai abinci wadda ta yi kokarin ta taimaka masa ya ga tsohon shuganan amma abin ya ci tura.   
Ya ce ya sauka ne a gidan sarkin Hausawan Abeokuta, Alhaji Ibrahim Hassan, ya yi jiyar kwana uku, sannan ya dauki keke ya kama hanya har gidan Obasanjo amma masu gadi suka hana shi shiga, amma da ya nuna musu takarda daga jam’iyar APC sai suka ba shi lokaci ya koma, amma da ya koma labarin bai canza ba. A karshe Abdullahi ya ce “bayan na kwan 9 a Abeokuta sai na sayar da kekena a wajan na yi kudin mota na koma gida”.
Bayan ya koma gida ya gaya wa Aminiya a waya cewa “Da zuwana gida ciwo ya kama ni sai da na kwana uku a daki ana yimin karin ruwa, laida hudu na sha. Na san kaddara ce kawai , na bar wa Allah komai”
Shi ko Adamu Muhammad wanda ya ce yana sana’ar saida Shanu a Tudun wada Kaduna, ,ya ce ya bar matarsa da ‘yaya 3 ne ya dauki hanya don yana san Obasanjo saboda rawar da ya ce tsohon shugaban ya taka a zaban shugaban kasa da ya gabata.
Ya ce ya yi kwana 25 a hanya, inda ya hadu da mutanen da suka yi masa kyauta saboda Obasanjo “hatta siturar da kake gani a jikina wani ne ya ba ni saboda shi. A gidan Sarkin Hausawan Abeokuta na sauka shi ma ya yi iya bakin kokarin sa dan ganin na cinma burina domin har sau 2 yana dauka ta a motarsa yana kai ni gidan bayan ni na jajje an hana ni shiga. ”.
Bayan wasu kwanaki ne sarkin ya sake dauka ta ya kai ni har cikin falon Obasanjo bayan sun gaisa ya fada masa dawowarsa ke nan daga kasar waje, zai huta mu yi masa uzuri mu dawo wani lokaci. Ni dai na yi Ido hudu da shi amma ban isar da sakon da na je da shi ba.
Ya ce ya koma ya yi takaicin hakan, domin ya shafe wata daya da sati biyu a Abeokuta yana so ya ga gwanin nasa amma abin ya ci tura.
Bayan da ya koma gidan sa a jihar Kaduna ya gaya wa Aminiya cewa “ina kokarin yin wamka na yanke jiki na fadi nan fa na yi ta suma, likita ya ce sanyi  da zazzabin cizon Sauro ne ya buge ni. Haka na yi ta jiyya ana ba ni magunguna da karin ruwa”.
Baya ga Sa’idu Abdullahi da Adamu Muhammad da suka yo tattakin akwai wadansu abokai guda 2 da suka shaida wa Aminiya cewa suma sun taso a kasa ne daga garin Kwantagorar jahar Neja don jinjina ga Obasnjo. Mutanen masu suna Nasiru da Muhammad Sani, sun samu labarin irin gwagwarmayar da Sa’idu da Adamu suka yi don ganin gwanin nasu amma hakan ya ci tura, hakan ya sa gwiwarsu ta yi sanyi domin ko yunkurin zuwa gidan ba su yi ba, bayan sun shafe kwana 25 a hanya. Nasiru ya zauna a gidan sarkin Hausawan Abeokuta na tsawon kwanaki 14 daga bisani ya bi Jirgin kasa ya koma gida, shi ko abokinsa Muhammad Sani sai da ya yi kwana 21, daga bisani ya ga haza ya koma inda ya fito.
Sarkin Hausawan Abeokuta Alhaji Ibrahim Hassan Hassan ya shaida wa Aminiya cewa ya yi iya kokarinsa don ganin masu tattakin sun cinma manufarsu sai dai hakan ya ci tura, domin a cewarsa, a wannan lokacin bai zauna a gida ba saboda shirya-shiryen rantsar da shugaban kasa. “Mutanen da suka yo tattakin sun yi abin da ya dace bisa la’akari da irin dattakon da Obasanjon ya nuna a dab da a yi zabe 2015”.