Masu tsafin kudi sun shiga hannu, fastonsu ya tsere

Bayan shigar matsafan hannun ’yan sanda, na ukunsu, wanda fasto ne a wani cocin zamani ne ya tsere.

Masu tsafin kudi sun shiga hannu, fastonsu ya tsere

’Yan sanda sun cafke wasu matsafa a yayin da suke tsaka da yin tasfin kudi ta hanyar amfani da makara a garin Benin na Jihar Edo.

Aminiya ta gano cewa bayan shigar matsafan hannun ’yan sanda, na ukunsu, wanda fasto ne a wani cocin zamani ne ya tsere.

Faston ya cika bujensa da iska ne bayan ya samu labarin cewa dubun abokan cin mushensa da suke tsafin kudin tare ta cika.

Matsafan wadanda shekarunsu 22 zuwa 24, sun shiga hannu ne a gidansu da ke yankin Irhirhi da ke kan titin Airport Road a garin Benin, hedikwatar Jihar Edo.

Makwabta ne dai suka tsegunta wa ’yan sanda, bayan sun ga matasan suna shigar da makara da mage da wasu kayan kulumboto tare da wasu mutane cikin gidan da suke haya.

Da jin haka ne ’yan sanda suka yi wa gidan dirar mikiya suka same su suna tsaka da tsubbace-tsubbacensu, inda bayan an kama su suka sanar cewa wani fasto ne na ukunsu.

Kakakin ’yan sandan Jihar Edo, Bello Kontongs, ya tabbatar da faruwar lamarin, da cewa matasan da aka kama ’yan asalin Jihar Delta ne.

Ya ce matasan sun shaida wa ’yan sanda cewa faston da suke yin tsafin tare ya tsere, amma ana gudanar da bincike domin shi ma a kamo shi.