Masu yamadidi kan shaidar karatun Buhari suna bata sunan kasarsu ne – ’Yankara

Wani manomi kuma dan kasuwa Alhaji Babangida Musa ‘Yankara, ya soki lamirin masu bata sunan kasarsu, inda suke yamadidi da cewa, Janar Muhammadu Buhari dan takarar shugabancin kasar nan a jam’iyyar APC ba shi da shaidar karatun kammala makaranta. A ganawar da ya yi da Aminiya, ya ce Babangida ‘Yankara ya ce, wannan abin kunya […]

Masu yamadidi kan shaidar karatun Buhari suna bata sunan kasarsu ne – ’Yankara
Masu yamadidi kan shaidar karatun Buhari suna bata sunan kasarsu ne – ’Yankara

Wani manomi kuma dan kasuwa Alhaji Babangida Musa ‘Yankara, ya soki lamirin masu bata sunan kasarsu, inda suke yamadidi da cewa, Janar Muhammadu Buhari dan takarar shugabancin kasar nan a jam’iyyar APC ba shi da shaidar karatun kammala makaranta. A ganawar da ya yi da Aminiya, ya ce Babangida ‘Yankara ya ce, wannan abin kunya ne da wasu suke fitowa suna bata sunan kasar haihuwarsu a idon duniya. Tun kafin Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya) ya fito ya kare kansa, na yi magana a kan wannan al’amari.

“Mutumin da ya rike mukamin Shugaban kasa da Gwamna da Minista da sauran mukamai, kuma shi ne ya tsaya takarar kujerar Shugaban kasa a shekarun 2003 da 2007 da 2011 ba a san cewa bai mallaki wannan takarda ba sai yanzu. Ya kamata mu rika girmama shugabanninmu amma ba kalamai marasa kan gado gare su ba,” inji shi.
Kuma ya shawarci masoya ‘yan takarar kujerar Shugaban kasa a zaben watan gobe da su tabbata cewa, sun zabi wanda suke so, tare da zabar ‘yan takarar kujerun majalisun tarayya da suka fito daga jam’iyya daya da za su ba shi hadin kai wajen gudanar da ayyuka ba tare da matsala ba.
Cikin hira da wakilinmu a Ibadan, Alhaji Babangida ‘Yankara ya ce, “akwai hadarin gaske dangane da zabar Shugaban da ya kasa samun wakilan majalisun tarayya masu rinjaye da za su rufa masa baya wajen aiwatar da ayyukan da ya yi wa jama’a alkawari. Misali, idan aka zabi Shugaba daga jam’iyyarsa, sannan aka zabi ‘yan majalisa daga wata jam’iyya daban, to kuwa babu wani ci gaba da za a samu sai ci gaban karuwar rikicin siyasa, wanda zai iya haifar da yunkurin tsige wannan shugaba saboda rashin rinjaye daga wakilan majalisu.”
“Idan muna so mu kauce daga fadawa cikin irin wannan matsala, to, ya kamata mu dawo daga rakiyar zaben shugaba daga jam’iya daban da ta ‘yan majalisa. Zabar dan takarar shugaban kasa da ‘yan majalisun tarayya da suka fito daga jam’iya daya shi ne zai yi maganin aukuwar rikicin siyasa a Najeriya. inji shi.