Masu ’ya’ya maza 13 da suke neman ’ya mace sun sake haihuwar namiji
Wadansu ma’aurata a garin Michigan da ke da ’ya’ya maza 13 kuma suna sa ran haihuwar ’ya mace, sun sake haihuwar namiji a matsayin da na 14 a ranar Laraba. Ma’auratan Jay da Kateri Schwandt, da ke Rockford, a Jihar Michigan ta kasar Amurka sun yi matukar mamaki yayin da suke fatan samun canji daga […]
Wadansu ma’aurata a garin Michigan da ke da ’ya’ya maza 13 kuma suna sa ran haihuwar ’ya mace, sun sake haihuwar namiji a matsayin da na 14 a ranar Laraba.
Ma’auratan Jay da Kateri Schwandt, da ke Rockford, a Jihar Michigan ta kasar Amurka sun yi matukar mamaki yayin da suke fatan samun canji daga haihuwar mazaje zuwa ’ya mace sai ga shi sun sake samun da namiji mai suna Finley Sheboygan, ma’auratan dai sun dade suna jiran sabon jaririn.
Mahaifin yaron Jay mai shekaru 43 ya fada wa jama’a cewa da sun samu haihuwar ’ya mace da sun fi hakan farin ciki, ‘amma tunda mun samu da namiji ba wai sabon abu ba ne, hakan ya sa wasu ma’aurata na neman namji mu kuma muke neman ’ya mace ruwa ajallo.’
Jay, ya kara da cewa, ina murnar samun da namiji da zai kasance na 14 a matsayina na mahaifinsa.
Mun hadu sosai lokacin bikin samun karuwarmu da da na 13 don haka yanzu iyalinmu sun cika daidai ke nan wannan zai zama na karshe ke nan, inji Jay.