Masu yi wa ƙasa hidima za su karɓi N77,000 daga Fabrairu – Shugaban NYSC
Gwamnatin tarayya ta sanar da ƙarin kuɗaɗen alawus ɗin NYSC daga N33,000 zuwa N77,000 duk wata
Shugaban Hukumar yi wa ƙasa hidima ta Najeriya, NYSC Birgediya Janar Yusha’u Dogara Ahmed ya tabbatar wa mambobin shirin da suke aikin yi wa ƙasa hidima na shekara ɗaya cewa za su fara karɓar Naira 77,000 daga watan Fabrairu.
A daidai lokacin da aka sake duba mafi ƙarancin albashi da hauhawar farashin kayayyaki, gwamnatin tarayya ta sanar da ƙarin kuɗaɗen alawus ɗin daga N33,000 zuwa N77,000 duk wata, amma da dama sun nuna damuwarsu kan aiwatar da hakan.
- Gwamna Buni ya zama Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Tafkin Chadi
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 3 sun sace 24 a Zamfara
A shekarar bara wani jami’in shirin ya danganta jinkirin aiwatar da biyan kuɗin da rashin kuɗi.
Amma yayin da yake bayani ga mambobin rukunin 2024 Batch ‘C’ Stream II a Jihar Katsina, Ahmed ya tabbatar da cewa an shigar da ƙarin kuɗin a kasafin kuɗin 2025.
Ya ce za a fara aiwatar da shi da zarar an zartar da kasafin kuɗin.
“Tuni gwamnatin tarayya ta amince da ƙarin kuɗaɗen alawus ɗin ku. Ba sabon labari ba ne; abin da muka amince ne da hannunmu. Abin da muke jira shi ne kawai aiwatar da kasafin kuɗin.
“Wannan watan (Janairu) ya riga ya ƙare, amma da zarar an gama kasafin kuɗin, nan da wata mai zuwa (Fabrairu), za ku fara karɓar Naira 77,000 maimakon N33,000 da aka saba karɓa.” In ji shi.