‘Masu yi wa yazawa cirar gaggawa na lalata mana kasuwanci’
Harkar dasa yazawa (kashu) da ’yan asalin Abuja ke yi a gonakinsu don samun diyyar fili kafin karbewa a yi aiki, yana jawo musu karin kudin shiga. Sai dai lamarin na fuskantar cikas a yanzu sakamakon cirar gaggawa da ake yi wa yazawan kafin ya kosa. Aminiya ta zanta da Alhaji Nuhu Usman Beldum, wani […]
Harkar dasa yazawa (kashu) da ’yan asalin Abuja ke yi a gonakinsu don samun diyyar fili kafin karbewa a yi aiki, yana jawo musu karin kudin shiga. Sai dai lamarin na fuskantar cikas a yanzu sakamakon cirar gaggawa da ake yi wa yazawan kafin ya kosa. Aminiya ta zanta da Alhaji Nuhu Usman Beldum, wani da ke sayan yazawa daga hannun manoma, don sayar wa masana’antu, inda ya yi bayani a kan matsalar.
Wane hali harkar yazawa ke ciki yanzu?
Gaskiyar magana ita ce, harkar ta fuskanci koma baya. A can baya mukan samu baki da ke zuwa su sayi yazawa a hanunmu, mu masu tarawa mu fitar zuwa kasar waje. Sai dai a yanzu hakan ya kau sakamakon yadda manomansa ke yi masa gaggawa su cire shi kafin ya kosa. An fi son a bar yazawa a jikin bishiyarsa har ya fado kasa da kansa, sai a tsinke kwallon. Sai dai kamar masu injin sarrafa yazawa na zamani suna iya markada shi don lemon jiws ko wani abu daban. To a haka sai a samu yazawa ya gama girma kuma ko da ya bushe yana nan da nauyinsa saboda man da ke ciki, sabanin danye wanda ruwa ne kawai a ciki yana bushewa sai ya yankwane kuma ko an dora shi a kan sikeli ba ya nauyi. Hakan ya sa yazawa ba inganci kuma a dalilin haka manyan dillalan da ke kai shi kasar waje ke asara saboda masu bukatarsa don sarrafawa ba sa saya. Muna fuskantar wannan matsala ce, tun daga wajen wadanda muke saye a hannunsu, wadanda yawanci a kauyukan da ke kewaye da birnin Abuja a Karamar Hukumar Birnin Abuja (AMAC) da Bwari da Kuje suke. A jihohin kuma da muke saya akwai Nasarawa da Neja da Kaduna.
Mene ne dalilin da ke sa a cire shi danye
Matsalar ta fi faruwa ce a nan Abuja saboda yawanci ana shuka bishiyoyin ne don masu shi su samu diyyar filayensu daga hukuma ko kamfani idan aikin raya kasa ya biyo ta wajen, ba wai sun shuka ba ne don su samu cin gajiyarsa ba. Sannan mai gonar na cirar gaggawar ce don gudun kada barayi su riga shi girbi. Sai dai alhamdulillahi ayyukan wayar da kai da muke yi tare da sarakuna da hakimai da agajin da muke samu daga jami’an tsaro na Cibil difens da ’yan sanda da ’yan banga sun sa matsalar ta ragu. Sai dai duk da haka masu zuwa su saya daga wajenmu sun ki dawowa saboda sun gano wasu sababbin kasuwanni a yankunan Ogbomosho da ke Jihar Oyo da Edo Kogi da Kwara wadanda sun jima tare da sanin ka’idar harkar. Su sun dauki shuka yazawa a matsayin sana’a, sukan sayi fili su shuka su samar da matakan tsaro. Kai in takaice maka mai gonar yazawa a wadancan jihohi shi ne mai arziki a tsakanin manomansu, sabanin namu da suka shuke shi ba tsari don kawai su samu cin gajiyar diyyar fili, kafin su gano amfaninsa daga baya.
Wace asara hakan ke jawowa?
Asarar tana da yawa. A bara mun sayi tan guda na yazawa a kan Naira dubu 500 zuwa dubu 600, sai dai har yanzu ga su nan ba mu sayar ba, saboda masu zuwa su saya sun yanke kafa dalilin asara da suka yi aka ki sayen hajar daga hannunsu bayan sun kai waje. A bana mun fara sayen tan guda a kan Naira dubu 200, sai dai a yanzu ba ma saya ko da a kan Naira dubu 100. Mun ki sayen ne saboda duk wanda muka tara tun na bara ba a saya ba. Idan kuma lissafin kilo za a yi, a bara muna sayen kilo kan Naira 500 zuwa 550, wanda buhun garara irin na dibino ke cin kilo 100. Sai dai a bana da farko mun fara sayen kilon a kan Naira 200 sai ga shi yanzu kilon bai kai Naira 100 ba. A baya idan manyan dillalan da ke zuwa daga Legas ba su zo ba, mukan yi waya da su mu kai musu har can, sai dai a yanzu ba ma yin wannan kasadar saboda koda mun kai sai su bar mu da kayanmu mu rasa yadda za mu yi da shi.
Wane hali ma’aikatanku suka shiga?
Ma’aikatan da ke aiki a karkashina sun kasu kashi biyu, akwai ejan-ejan da nake ba su kudi su bazama dazuzzuka nemo yazawa. Akwai kuma leburorin da nake tare da su a nan da ke aiki a sito-sito hudu da nake da su. A kowane sito akwai ma’aikata 15 zuwa 20 da ke aikin sauke buhunan yazawa daga mota da tantace kwayar da auna shi a kan sikeli da sake shirya shi bayan an saya, sai kuma a dora shi a kan babbar mota idan za a tafi da shi zuwa Legas. Sai dai a bana sito 2 ne kadai ake aikin kuma leburorin gaba daya ba su wuce bakwai ba. Bangaren ’yan kasuwa kuma da nake ba su kudi su nemo yazawa, a bara na yi hulda da mutum sama da 100 da na ke rarraba wa kudi su nemo yazawa daga kauyuka da gonaki, sai dai a yanzu ba su wuce mutum shida ba.
Me ya sa ake sayo marar kyau?
Bahaushe ya ce idan dambu ya yi yawa ba ya jin mai. Muna jan kunnen yaranmu a kan su guji sayen marar inganci da kuma sanar da su irin wadanda muke bukata. Sai dai wadansu daga cikinsu idan suka sayi mai kyan idan suka ci karo da mummuna shi ma sai su sayi wani adadi su surka. Kai kuma da ya kawo maka dama kudi ka ba shi, idan ka ki karba ba ka san ranar da kudinka zai fito ba, sai dai ka karba hakan daga baya sai ka daina hulda da shi. Bayanin da muka samu shi ne a dalilin wannan matsalar kasar Bietnam kadai a bara ta ki sayan yazawa daga Najeiya da adadinsa ya kai tirela 300, bayan an kai can. Kuma hakan ya ci gaba da faruwa ne sakamakon ci gaba da sayan yazawa marar inganci da wasu manyan dillalai daga wasu yankunan ke yi. Wato idan suna da yazawa mai kyau kamar tirela 4 sai su sayi mara kyau tirela daya su surka ya saje. Sai dai idan aka kai waje, sai na’ura ta tantance kuma a sanadin haka sai a ki saye. Sai dai a yanzu zan iya cewa harkar ta gyara kanta da kanta saboda su kansu masu cirar gaggawar ko satar, sun ga illar kin sayenta, idan sun ciri danye ba mai saya sakamakon haka abin sai ya yi sauki, sai dai kuma har yanzu masu sayen sun ki dawowa.
Yaya mu’amala tsakaninku da hukuma?
A baya dai ba wata hulda da ke tsakaninmu. Ma’ana ba su ba mu wani tallafi, kuma ba sa damunmu da wani haraji. Sai dai a yanzu mun fara shigarsu kuma daga baya-bayan nan mun yi zama da Bankin NEDIM, Wato bankin da ke tallafa wa harkar fitarwa da shigo da kayan da ake bukata, mun zauna da su mun tattauna. Haka nan su ma wadansu shugabannin kananan hukumomin Abuja mun yi zama da su mun kuma tattauna abin da ya shafi tsaro da yadda za a tabbatar da ingancin yazawar.