Masu yin jabun kudi da miyar waken soya sun shiga hannu a kasar Sin
Jami’an ‘yan sandan kasar Sin sun kama masu yin kudin jabu da miyar waken soya a garin Weicheng da ke gabashin Sin, a lardin Shandong. Jami’an tsaron sun kama mutumn 245 dagha cikin gungun masu sarrafa jabun kudinMafi yawan masu yin kudin suna mu’amala ne ta shafukan sadarwar intanetSun, daya daga miyagun da ake tsare […]
Jami’an ‘yan sandan kasar Sin sun kama masu yin kudin jabu da miyar waken soya a garin Weicheng da ke gabashin Sin, a lardin Shandong. Jami’an tsaron sun kama mutumn 245 dagha cikin gungun masu sarrafa jabun kudin
Mafi yawan masu yin kudin suna mu’amala ne ta shafukan sadarwar intanet
Sun, daya daga miyagun da ake tsare da su, ya bayyana wa ’yan sanda cewa, ya sayi jabun kudin Yuan 20 daga wani da suka hadu da shi ta intanet. A lokacin a akwai matsala daya da ta dame shi, domin kudin sabuntar su ta yi yawa. Sai ya tuna a bara ya taba sayen irin wadannan kudi daga wurin mutumin da ya hadu da shi a intanet, sai ya tsoma su cikin miyar waken soya, don su tsufa. Don tsufan kudi ke bayar da damar a shigar da su cikin sauki.
Tun daga lokacin sai Sun ya bude harkarsa ta buga jabun kudi, inda yake sarrafa su da miyar wake. Sai dai Sun ya ce an tursasa shi ne ya yi aiki tare da gungun masu yin jabun kudi.
A sanadin binciken da jami’a tsaro suka yi wa Sun, sun kama masu aikata laifi har mutum shida da ked a rassa a kasar Sin, sannan suka kwace kudin da yawan su ya kai Yuan miliya daya (wato daidai da Dala dubu 152) ; kimanin Naira miliyan 41,192,000.