Masu yin NYSC 1,130 ne suka koyi sana’o’in hannu a Yobe

Kimanin Matasa masu yi wa kasa hidima na NYSC su dubu 1,130 da suke hidimar kasa a jihar Yobe a rukunin B na shekarar 2019 ne suka koyi sana’oi’n hannu daban daban a karkashin shirin ‘SAED Skills Aquasition and Empowerment Development’. Da take jawabi a wajen rufe taron bada horon Kodinetan ‘yan yi wa kasar […]

Masu yin NYSC 1,130 ne suka koyi sana’o’in hannu a Yobe

Kimanin Matasa masu yi wa kasa hidima na NYSC su dubu 1,130 da suke hidimar kasa a jihar Yobe a rukunin B na shekarar 2019 ne suka koyi sana’oi’n hannu daban daban a karkashin shirin ‘SAED Skills Aquasition and Empowerment Development’.

Da take jawabi a wajen rufe taron bada horon Kodinetan ‘yan yi wa kasar hidima ta jihar Yobe Misis Grace J Adzer, a sansanin su na wucin gadi da ke garin Potiskum, cewa ta yi shirin ana yin shi ne dan koyawa ‘yan yi wa kasa hidima sana’oin dogaro da kan su.

Ta ce, sana’oi’n yana zama musu garkuwa daga zaman banza idan basu samu aikin yi ba bayan kammala hidimar kasar da suke yi na shekara guda.

Misis Grace, ta kara da cewa matasa an koya musu sana’oi daban daban ne dan ci gaban rayuwar su.

A nasa jawabi tun farko shugaban shirin na SAED na NYSC Ibrahim Margina Ishidi, cewa ya yi Matasan sun sami horo akan sana’ar na’ura mai aiki da hasken rana ta solar da koya musu daukar hoto marar motsi da yin sarka da dinki da abun wuya na mata da yin takalma da ilimin kimiyyar sadarwa ICT da sauran su.

Wasu Matasa ‘yan yi wa kasar hidima da suka koyi sana’oin sun yabawa Hukumar NYSC bisa tarbiya da kuma sana’a da suka koya musu a lokacin da suke yi wa kasar su hidima inda suka yi alkawarin dorawa daga inda aka koya musu.

Wata matashiya Olaiya Faith, daga jami’ar tarayya ta Abeokuta da ta koyi daukar hoto ta ce, idan ta koma garin su za ta ci gaba da sana’ar daukar hoto da ta koya saboda sana’a ce.

“Tayi matukar godewa Gwamnatin Tarayya da Hukumar NYSC kan bullo da shirin SAED skills Acqusition and Empowerment Development”. Wasu daga cikin Matasa sun baje kolin fasahar abubuwan da suka koya a sansanin nasu na wuci gadi da ke garin Potiskum a jihar ta Yobe.