‘Masu yin zanga-zangar sace Leah Sharibu na jawo mata karin fitina ne’
Wani Dan rajin kare hakkin jama’a kuma Dan jarida da ke aiki a gidan Talabijin na kasa NTA, Malam Hussaini Isa, ya yi suka a kan aiwatar da zanga-zanga a matsayin bangare na neman a sako Leah Sharibu da wasu suka aiwatar a ranar Laraba, don tunawa da ranar da a ka sace ta. Leah […]
Malam Hussaini Isa a tsakiya sai mahaifiyar Leah Sharibu daga hagu da kuma wata goggonta a yayin daya daga cikin ziyarar
Wani Dan rajin kare hakkin jama’a kuma Dan jarida da ke aiki a gidan Talabijin na kasa NTA, Malam Hussaini Isa, ya yi suka a kan aiwatar da zanga-zanga a matsayin bangare na neman a sako Leah Sharibu da wasu suka aiwatar a ranar Laraba, don tunawa da ranar da a ka sace ta.
Leah Sharibu, wadda ‘Yan Kungiyar Boko Haram suka sace tare da wasu dalibai ‘yan makarantar sakandaren ‘yan mata da ke garin Dapci a jihar Yobe, ta cika shekara 2 a yau Laraba a hannun masu garkuwa da ita din.
Kamar yadda a ka ruwaito tun bayan sako ragowar ‘yan matan, ‘yan Kungiyar sun ce sun riketa ne kan kin yarda da watsi da addininta na Kirista, da kuma karban na musulunci kamar yadda suka bukata.
Malam Hussaini Isa, wanda ya wallafa bukatar a shafinsa na facebook, ya ce yin zanga-zangar da wasu suka shirya a yau, tare da yin kira ga gwamnati da ta kara azama kan neman a saki yarinyar, tamkar suna kira ne ga ‘yan Boko Haram su kara adadin kudi da suke nema a matsayin na fansa ne.
“A dalilin aikina a gidan talabijin na NTA na ziyarci iyayen Leah Sharibu har sau 6. “A saboda haka na san irin zafin da suke ji idan rana irin wannan ta zagayo.
“Amma babban abin da ya kamata mu yi shi ne ci gaba da yi mata addu’a tare da sauran wasu da dama da aka kamata irin wannan hanyar na tsawon shekaru.
“Wasu daga cikinsu sun shafe sama da shekara 8 a hannun ‘yan Kungiyar, amma ba tare da bayanansu ya bayyana ba irin nata, watakila saboda rashin karfi, ko matsayi ko kuma wadanda su tsaya a kan lamarinsu.
“Hanyar hulda da mutane irin Boko Haram ita ce, kauracewa yayata wadanda suka ka sace. “Aiwatar da akasin hakan, sharrinsa na iya fin alherinsa ni a ganina,” in ji malam Hussai