Masu zanga-zanga a Sifen sun bukaci rusa masarautar kasar

A ranar Talata wasu dubban masu zanga-zanga a kasar Spain sun bukaci gwamnatin kasar ta gudanar da zaben jin ra’ayin jama’a, wanda zai ba su damar zaben rusa masarautar kasar ko barinta.Wannan bukatar na zuwa ne bayan matakin Sarkin Spain, Juan Carlos na bayyana aniyarsa ta sauka daga sarauta don ya baiwa dansa, Yarima Felipe […]

Masu zanga-zanga a Sifen sun bukaci rusa masarautar kasar
Masu zanga-zanga a Sifen sun bukaci rusa masarautar kasar

A ranar Talata wasu dubban masu zanga-zanga a kasar Spain sun bukaci gwamnatin kasar ta gudanar da zaben jin ra’ayin jama’a, wanda zai ba su damar zaben rusa masarautar kasar ko barinta.
Wannan bukatar na zuwa ne bayan matakin Sarkin Spain, Juan Carlos na bayyana aniyarsa ta sauka daga sarauta don ya baiwa dansa, Yarima Felipe damar maye gurbinsa. Sarkin mai shekara 73, ya shafe shekara kusan 40 a kan sarauta. Amma bai bayyana ranar da zai sauka ba tukuna.
Bugu da kari, kimar sarkin ta ragu a idon ’yan kasar saboda zargin almundahana da ake masa. Cikin abubuwan da suka kara masa bakin jini, har da wani yawon bude ido da ya je kasar Botswana, wanda lokaci kasar na cikin matsin tattalin arziki. A lokacin balaguron ya samu rauni a kwankwaso, wanda kuma ba tare da wata-wata ba aka dawo da shi kasar don jinya.