Masu zanga-zanga su zo mu buɗe ƙofar sulhu —Tinubu

Na ji ciwon irin asarar rayuka da aka yi a jihohin Borno, Jigawa, Kano, Kaduna da sauransu.

Masu zanga-zanga su zo mu buɗe ƙofar sulhu —Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga masu zanga-zangar tsadar rayuwa a fadin Nijeriya da su dakata haka su zo a buɗe ƙofar tattaunawa da sulhu.

Shugaban ya yi wannan kiran ne ranar Lahadi a jawabin da ya yi wa ’yan Nijeriya ta gidan talbijin na ƙasa, kwanaki huɗu bayan ’yan ƙasar sun tsunduma cikin zanga-zanga kan tsadar rayuwa.

Shugaban, wanda ya jajanta wa wadanda suka rasa rayukansu da iyalansu, ya kara da cewa ya zama wajibi a tabbatar da zaman lafiya a tsakanin jama’a.

Tinubu ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta zuba ido wajen barin “wasu tsiraru masu ɓoyayyiyar manufa ta siyasa su wargaza wannan ƙasa mai albarka ba.”

“A matsayina na shugaban wannan ƙasa, wajibi ne na tabbatar da doka da zaman lafiya kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar nan ya ɗora min alhakin hakan kuma na amince, da cewa zan kare rayuka da dukiyoyin kowane ɗan ƙasa.

“A wannan yanayi da ake ciki, ina ba masu shirya wannan zanga-zangar da ma masu gudanar da ita umarni, da su dakatar da duk wata zanga-zanga, su maye gurbinta da buɗe ƙofar tattaunawa da sulhu, wanda a ko da yaushe ƙofata a buɗe take ga hakan.

“Na ji ciwon irin asarar rayuka da aka yi a wasu jihohi, irin su Borno, Jigawa, Kano, Kaduna da dai sauransu, da ɓarnata dukiyoyin jama’a a wasu jihohin, kai har ma da yadda aka riƙa wawushe manyan kantuna da shaguna, saɓanin alƙawarin da masu shirya zanga-zangar suka yi cewa, zanga-zangar za ta kasance cikin lumana a faɗin ƙasarmu.

“Wannan asarar dukiya da ɓarna da aka yi a wadannan wurare sun kara mayar da hannun agogo ta fuskar ci gabanmu.”

A karon farko Tinubu zai tattauna da ’yan Najeriya kai-tsaye

Zazzaɓin Lassa: Mutum 190 sun mutu, 1,154 sun kamu a 2024 – NCDC

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume