Masu zanga-zanga sun bijire wa dokar hana fita a Jigawa

Jami’an tsaron ba za su iya tabbatar da an kiyaye da doka da oda na tsawon lokaci ba.

Masu zanga-zanga sun bijire wa dokar hana fita a Jigawa

An shiga rana ta biyu ta zanga-zangar tsadar rayuwa a wannan Juma’ar a wasu sassan Dutse, babban birnin Jihar Jigawa.

Wannan dai na zuwa ne a yayin da masu zanga-zangar suka bijire wa umarnin gwamnatin jihar wadda tun a jiya Alhamis ta sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24.

A halin yanzu dai jami’an tsaro sun sanya shigayen datse masu zanga-zangar a yankin Zai na birnin Dutse domin hana su shiga yankunan kasuwanci da ke ɗauke da manyan ma’aikatu da shagunan ’yan kasuwa.

A cewar ɗaya daga cikin mazauna unguwar Zai, dubban matasan sun mamaye tituna da dama suna waƙe iri daban-daban ciki har da kiraye-kiraye na gayyatar sojoji su karɓe akalar jagorancin ƙasar.

Mazaunin wanda ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce fusatattun matasan na ci gaba da gudanar da zanga-zangar ce duk da tarnaki na barkonon tsohuwa da jami’an tsaro ke jefa musu a ƙoƙarin tarwatsa su.

Wani da lamarin ke wakana a kan idonsa ya tabbatar da cewa kawo yanzu jami’an tsaron sun cafke gomman matasa cikin har da yara maza masu ƙananan shekaru.

A garin Gumel kuwa, tarzoma ta lafa a yayin da jami’an tsaro sun yi shirin-ko-ta-kwana tare da kafa shingaye a duk wasu manyan tituna.

Sai dai wata majiya ta ce ana zaman ɗarɗar la’akari da cewa adadin jami’an tsaro da aka tanada ya yi ƙarancin da ba za su iya tabbatar da an kiyaye da doka da oda na tsawon lokaci ba.

An ceto jaririyar da ’yar aikin gida ta sace a Edo

An ceto mutum 58 da aka sace a Kaduna

Sarkin Zazzau ya naɗa sabbin hakimai 7

Hajjin 2025: Maniyyata za su fara ajiye N8.4m a Kaduna