Masu zanga-zanga sun bukaci sojoji da su sauka

Jami’an tsaron kasar Sudan sun kai wa masu zanga-zangar neman su  mika mulki ga farar hula hari, wadanda ke wajen hadkwatar sojan kasar a Khartum babban birnin kasar. An jiwo karar harbe-harben bindiga, inda jami’in kiwon lafiya suka ce akalla mutane 13 ne aka kashe, wasu da dama kuma suka sami raunuka, tun bayan hambarar […]

Masu zanga-zanga sun bukaci sojoji da su sauka

Jami’an tsaron kasar Sudan sun kai wa masu zanga-zangar neman su  mika mulki ga farar hula hari, wadanda ke wajen hadkwatar sojan kasar a Khartum babban birnin kasar.

An jiwo karar harbe-harben bindiga, inda jami’in kiwon lafiya suka ce akalla mutane 13 ne aka kashe, wasu da dama kuma suka sami raunuka, tun bayan hambarar da Gwamnatin Omar Al-Bashir, a watan Afrilu sojoji ke rike da madafun ikon kasar, sai dai sojojin sun karyata cewar sun yi amfani da karfi a kan masu zanga zangar.

Shugaban Masu zanga-zangar yace sun dakatar da duk wata tautaunawa da sojojin kasar, har sai sun mika mulki ga farar hula, inda ya yi kiran a yi yajin aikin gama gari.

Tawagar kwamitin likitocin kasar ta Sudan, wadda take kusa da masu zanga-zangar ta ce mutane 13 ne aka kashe kuma wasu da dama suna cikin halin kaka-n-kayi saboda raunukan da suka samu a dalilin harin na sojoji.