Masu zanga-zanga sun fara kiran Shugaban Sudan ya yi murabus
Dubban masu zanga-zanga a kasar Sudan sun fara kiran Shugaba Omar Hasan al-Bashir ya yi murabus.Sannan shugabannin manyan jam’iyyun adawa na kasar da suka hada da National Umma Party (NUP) ta Sadik al-Mahdi da Popular Congress Party (PCP) ta Hassan al-Turabi sun fito fili suna kira ga magoya bayansu su shiga cikin zanga-zangar wadda aka […]
Dubban masu zanga-zanga a kasar Sudan sun fara kiran Shugaba Omar Hasan al-Bashir ya yi murabus.
Sannan shugabannin manyan jam’iyyun adawa na kasar da suka hada da National Umma Party (NUP) ta Sadik al-Mahdi da Popular Congress Party (PCP) ta Hassan al-Turabi sun fito fili suna kira ga magoya bayansu su shiga cikin zanga-zangar wadda aka shafe sama da mako daya ana gudanar da ita a wasu sassan kasar Sudan, sakamakon janye tallafin man fetur da gwamnatin kasar ta yi.
Janye tallafin man fetur da Sudan ta yi a makon jiya ya hadu da gagarumar adawa, ta yadda hatta manyan ’ya’yan Jam’iyyar National Congress Party (NCP), mai mulkin kasar suka nuna adawa da shi.
A farkon wannan mako fiye da manyan jami’an jam’iyyar 30 da magoya bayanta sun aike da wasika ga Shugaba Omar Hassan al-Bashir suna neman ya dawo da tallafin man tare da aiwatar da sauye-sauyen siyasa da na tattalin arziki.
Dubban jama’a sun rika gudanar da zanga-zanga a titunan Khartoum suna fadin “Sai ’yanci” tare da nanata kiran Shugaban ya yi murabus bayan da aka kashe sama da mutum 50 a yayin zanga-zangar adawa da tsuke bakin aljihun gwamnati.
Gwamnatin Sudan ta sanya takunkumi ga kafofin watsa labarai, kuma ta bullo da wani shirin lallashin jama’a, inda ta ce za ta raba kudi ga rabin jama’ar kasar domin saukaka musu tsadar man fetur din da na kayan abinci.
Wannan ne zanga-zanga mafi muni a Sudan a shekara 24 na mulkin al-Bashir.
A ranar Lahadi da ta gabata masu zanga-zangar sun rika daga hoton Salah al-Sanhouri wanda aka bindige a ranar Juma’ar da ta gabata a garin Burri da ke tsohuwar gundumar Khartoum.
Wani dan uwansa, Ghazi al-Sanhouri ya ce, “Zanga-zangar za ta ci gaba har sai ta zama ta kasa baki daya. Za mu ci gaba da fallasa mugun shirin gwamnati na dakile zanga-zangar ta hanyar kisa da musgunawa.”
Mahaifin Al-Sanhouri, Moudasiir al-Reih, ya ce: “Wannan gwamnati ta yi kusan zuwa karshe… da yardar Allah za ta kawo karshe.”