Masu zanga-zanga sun hana zirga-zirgar ababen hawa a Zariya

An kusa hatsaniya tsakanin masu zanga-zangar da wasu sojoji da suka hana wucewa.

Masu zanga-zanga sun hana zirga-zirgar ababen hawa a Zariya

Masu zanga-zangar tsadar rayuwa ta EndBadGovernance sun hana zirga-zirgar ababen hawa a manyan tituna a garin Zariya da ke Jihar Kaduna.

Yayin da zanga-zangar ta shiga rana ta biyu, matasan sun datse wurare masu muhimmanci domin hana zirga-zirgar ababen hawa a kan manyan tituna.

Wakilinmu ya ruwaito cewa an toshe babbar hanyar nan da ta hada birnin Zariya zuwa Ƙofar Doka zuwa mahaɗar Agoro.

Hakazalika matasan sun tare hanyar Ƙofar Doka daura da mahaɗar Ɗan Magaji.

Bayanai sun ce an kusa hatsaniya a lokacin da matasan suka yi ƙoƙarin hana motocin sojoji wucewa a shatale-talen Ƙofar Doka, amma wasu masu jagorantar zanga-zangar sun sasanta lamarin, inda aka bude wa motocin hanya suka wuce ba tare da wata matsala ba.

Kazalika, shaguna da sauran wuraren kasuwanci sun kasance a rufe a faɗin garin.

Sai dai masu zanga-zangar sun sassauta harkokinsu a lokacin sallar Juma’a ta yadda aka bai wa musulmin damar shiga masallaci.

Aminiya ta ruwaito cewa, zanga-zangar ta kasance cikin lumana duk da cewa akwai ƙarancin jama’a idan aka kwatanta da ranar farko.

An ceto jaririyar da ’yar aikin gida ta sace a Edo

An ceto mutum 58 da aka sace a Kaduna

Sarkin Zazzau ya naɗa sabbin hakimai 7

Hajjin 2025: Maniyyata za su fara ajiye N8.4m a Kaduna