Masu zanga-zanga sun kai ziyara gidan Buhari a Daura

Jami’an tsaro ke faɗi-tashin ganin an kiyaye doka da oda a garin na Daura.

Masu zanga-zanga sun kai ziyara gidan Buhari a Daura

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Fusatattun masu zanga-zanga a wannan Alhamis ɗin sun ziyarci gidan tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari da ke garin Daura a  Jihar Katsina.

Masu zanga-zangar matsin rayuwar sun yi yunkurin kutsa kai gidan tsohon shugaban kasar suna kururuwar cewa an kai su bango a sanadiyar matsin tattalin arziki da aka tsinci kai a yanzu.

Sai dai wata majiya da Aminiya ta zanta da ita ta wayar tarho ta ce masu zanga-zangar sun yi ta kone-kone a kofar gidan tsohon shuban kasar.

Cikin wani bidiyo da Aminiya ta yi arba da shi ya nuna wasu matasa a kofar gidan tsohon shuugaban kasar suna ihun “Bama yi! Bama yi! Bama yi!.”

Sai dai daga bisani wasu mutane daga gidan sun fito suna hakurkurtar da masu zanga-zangar, inda suka nemi matasan su wakilta daya daga cikinsu da zai bayyana korafinsu kuma suka nadi sautin murya da hoton bidiyo tare da alkawarin cewa za su isar da sakonsu ga tsohon shugaban kasar.

Rahotanni sun ce daga nan kuma matasan suka nufi fadar mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Farou Umar Farouk, inda suka fuskanci tirjiya daga ɓangaren jami’an tsaro.

Ana fargabar cewa jami’an tsaro sun harbi ɗaya daga cikin masu zanga-zangar da suka yi yunƙurin kutsa kai gidan sarkin.

Wata majiya ta ce ta lura da yadda masu zanga-zangar suka yi ɗan ƙaramin ta’adi a gidan Magajin Garin Daura, Alhaji Musa Uba, wanda ɗaya ne daga cikin manyan masu riƙe da sarautar gargajiya a garin.

A cewar majiyar, Magajin Garin na Daura na ɗaya daga cikin masu adawa da zanga-zangar tsadar rayuwar da ake yi a faɗin ƙasar.

Sai dai majiyar ta ƙara da cewa a halin yanzu tarzoma ta lafa yayin da jami’an tsaro ke faɗi-tashin ganin an kiyaye doka da oda a garin na Daura.

Tuni dai wasu jihohin Nijeriya suka saka dokar hana zirga-zirga bayan da zanga-zangar da aka fara ranar Alhamis a faɗin ƙasar ta rikiɗe ta koma tarzoma da fasa shaguna, kayayyaki, da gine-ginen gwamnati, har ma da asarar rayuka.