Masu zanga-zanga sun tare babbar hanyar Abuja kan matsalar tsaro

Masu zanga-zangar sun nemi gwamnati ta kawo ƙarshen matsalar tsaro a ƙasar.

Masu zanga-zanga sun tare babbar hanyar Abuja kan matsalar tsaro

Zanga-zangar da ake yi kan matsalar rashin tsaro a Babban Birnin Tarayya, Abuja ta shiga rana ta uku, inda ɗaruruwan matasa suka tare babbar hanyar shiga birnin.

A ranar Asabar, masu zanga-zanga sun tare gadar da ke kan hanyar Karu zuwa Nyanya, wacce ta haɗa Abuja da Jihar Nasarawa.

Masu zanga-zangar na neman a inganta tsaro saboda yawaitar sace-sacen mutane da hare-hare.

Sun riƙe kwalaye masu rubutu tare da rera waƙoƙi suna zanga-zanga, suna cewa gwamnati dole ta ƙara ƙaimi wajen kare rayuka da dukiyoyi.

Sun taru a kan gadar yankin, sannan daga baya suka yi tattaki zuwa Nyanya.

Wannan ya jawo cunkoson ababen hawa a kan hanyar Abuja zuwa Keffi, inda matafiya da dama suka maƙale na tsawon sa’o’i.

Masu zanga-zangar sun ce rayuwa ta yi wahala saboda rashin tsaro, kuma sun buƙaci gwamnati ta ɗauki matakan gaggawa.

An tura jami’an tsaro domin sanya ido da kuma kula da zirga-zirgar ababen hawa.

An kuma shawarci direbobi su bi wasu hanyoyi daban.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a samu rahoton tashin hankali ko raunuka ba, amma an tare hanyar lamarin da kawo tsaiko ga masu ababen hawa.