Ana zanga-zangar neman tura sakamakon zabe ta intanet ta barke a Majalisa

A makon jiya ne kura ta tashi bayan bullar labarin cewa majalisar ba ta amince da tura sakamakon zabe kai tsaye ta intanet ba.

Ana zanga-zangar neman tura sakamakon zabe ta intanet ta barke a Majalisa

Masu neman tabbatar da dokar tura sakamakon zabe ta intanet daga rumfunan zabe, sun mamaye harabar Majalisar Dokoki ta Kasa domin tanadin dokar ya samu shiga.

Hakan na zuwa ne a yayin da majalisar ke shirin gudanar da zama na gaggawa kan sauye-sauyen da aka yi wa dokar zabe kafin su fara aiki gabanin babban zabe na 2027.

Tsohon dan takarar shugaban kasa a Jam’iyyar LP kuma jigo a Jam’iyyar ADC, Peter Obi da kuma ’yar gwagwarmaya Aisha Yesufu suka shiga cikin masu zanga-zangar ta safiyar Litinin.

Peter Obi ya bayyana cewa ’yan Najeriya ba za su lamunci bata lokaci wurin tura sakamakon zabe ko kuma uzurin rashin kyan layin sadarwar intanet kafin tura sakamkon zabe ba, yadda aka fuskanta a zabukan baya.

“Abin da muke so shi ne tarin zabe da ake yin komai a fili daga farko har karshe. Muna so a yi wa dokar zabe gyara ta yadda zabuka za su kasance masu ingnaci da karbuwa ga ’yan Najeriya,” in ji shi.

A makon jiya ne kura ta tashi bayan bullar labarin cewa majalisar ba ta amince da tura sakamakon zabe kai tsaye ta intanet ba.

A kan haka ne bangaren marasa rinjaye a majalisar suka nesanta kansu da hakan a yayin da sauran ’yan Najeriya suka tashi haikan domin ganin an tabbatar da tsarin tura sakamakon zabe kai tsaye ta hanyar amfani da na’ura.

Yawanci ana ganin yin hakan zai takaita magudin zabe, musamman abubuwan da suka danganci aringizon kuri’a.

Aminiya ta ruwaito cewa an jibge jami’an tsaro—’yan sanda NSCDC—da motocinsu a zagaye da kuma muhimman wurare domin tabbatar da doka da oda.