Masunci ya kama kifi mai fuskar mutum
Wani mai nazarin kimiyya a Cibiyar Marine Stewardship Council da ke kasar Indonesiya mai suna Dokta Dabid Shiffman ya bayyana gano wani kifi mai fuskar mutum da wani masunci ya kama. Dokta Shiffaman ya bayyana wannan kifi a matsayin wata halitta da ake samu bayan haifar jinsin dan Adam ko dabba, ta yadda idan aka […]
Wani mai nazarin kimiyya a Cibiyar Marine Stewardship Council da ke kasar Indonesiya mai suna Dokta Dabid Shiffman ya bayyana gano wani kifi mai fuskar mutum da wani masunci ya kama.
Dokta Shiffaman ya bayyana wannan kifi a matsayin wata halitta da ake samu bayan haifar jinsin dan Adam ko dabba, ta yadda idan aka samu akasin rabuwar aikin kwakwalwa waje biyu don yin aikin da ya kamata da masana ke kira da Cyclopia.
- Shugaban Tanzania John Magufuli ya rasu
- Ahmad Lawan ya roki Saudiyya ta sako ’yan Najeriya 10,000 da ta tsare
- ’Yan bindiga na samun taimako daga kasashen waje —NSCDC
Kifin, jinsin Shark, da masuncin ya gano, ya ba masuncin mamaki bayan kama kifin a bakin tekun kasar Indonesiya.
Masuncin mai suna Abdullah Nuren ya sa komarsa a cikin ruwa a yankin Rote Ndao a Lardin Nusa Tenggara ta Gabas a ranar Lahadi 21 ga Fabrairun bana.
Abdullah ya yi katarin kama kifi mai juna biyu a lokacin da yake sana’arsa ta kama kifi sai wannan kifin mai fuskar mutum ya fice daga cikin sauran kifayen ya fada cikin kwale-kwalensa.
Wadansu masana sun ce, ba kasafai ake samun irin wannan halitta ba inda bayan Abdullah mai shekara 48 ya yanka cikin kifin ya ga ’ya’ya biyu, amma sai na uku ya fice.
Daya daga cikin ukun na da wata halitta ta daban saboda idonsa biyu suna zagaye da hancinsa a kasa kamar yadda wani bidiyo da Abdullah ya wallafa ya nuna kifin a cikin wani akwati.
Kifin mai fuska irin ta mutum yana da ido a hannun dama a kasan hancinsa, maimakon gefe guda kamar yadda sauran halittu masu rai suke.
Yana da baki a bude, inda kamanninsa ke nuna kamar fuskar mutum. Abdullah ya kara da cewa: “Da farko na ga uwar kifin Shark a cikin rariyar kama kifi ta jirgin.
“Bayan gari ya waye, sai na farke cikin kifin, daga nan na gano tana dauke da jariran kifi uku a cikinta.
“Jarirai biyu suna kama da uwar kifin, sai daya kuma na da irin fuskar mutum.”
Dokta Dabid Shiffman ya ce, yanayin halittar wannan kifi ta samu aibi ne daga haihuwarsa.
Ya ce: “Wannan ba abu ba ne da na yi nazari a kansa ba, amma wadansu masana sun ce, hakan na faruwa ne sanadiyyar wani akasi daga kwakwalwa (Cyclopia).
Masunci Abdullah ya ce, “Ya dauki kifin mai irin fuskar mutum zuwa wajen ’yan uwansa don adana shi. “Wani makwabcina ya bukaci in sayar masa da kifin, amma na ki amincewa,” inji shi.
Abdullah ya kara da cewa, “Gidan ya cika da cincirindon mutane da suka zo don ganin kifin.”
“Wadansu mutane da yawa sun bukaci na sayar masu, amma zan adana shi ne. “Ina tunanin zai kawo min nasara nan gaba,” inji shi.