Masunta sun ceto matar da ta bace shekara biyu baya a raye cikin teku
“Na gode wa Ubangiji da nake raye, sannan Ya tsawaita rayuwata.
An ceto wata mata mai suna Angelica Gaitan da aka sanar da bacewarta shekara biyu da suka wuce, bayan ruwa ya kwararo ta gabar tekun Arewacin kasar Colombia a makon jiya.
An gano Angelica a cikin tekun sama da nisan mil daya a birnin Puerto Colombia, kafin daga bisani a kawo ta gabar tekun ta fara karbar magani.
- Magidanci ya rataye kansa bayan ya harbe matarsa
- Kotu ta yanke wa Donald Trump da Sarki Salman hukuncin kisa
Jaridar La Libertad ta kasar ta wallafa cewa, wadanda suka ceto matar da farko sun yi biris da matar bayan ganinta tana watangaririya a saman ruwa, sai da ta kai ga daga hannunta don neman agaji daga wurinsu.
A wani hoton bidiyo da Rolando Bisbal ya dauka an nuna daya daga cikin masuntan da suka ceto Angelica kuma bayan fitar da ita daga cikin tekun an dora ta a cikin kwale-kwale bayan ya fito da ita an zaunar da ita a kan kujera a gefen tekun.
A cikin bidiyon da aka nada, an nuna Angelica Gaitan ba ta cikin hayyacinta sakamakon halin da ta tsinci kanta.
Misis Angelica Gaitan ta bayyana wa gidan rediyon Kwalombiya cewa, “An gano ni ina ta watangaririya a saman teku ba na cikin hayyacina a lokacin,” kamar yadda masunta da suka hada da: Mista Bisbal da abokanansa suka sanar.
“Na gode wa Ubangiji da nake raye, sannan Ya tsawaita rayuwata.
An kawo ni cibiyar kiwon lafiya, inda ake kula da lafiyata da abin da suka dace a yi min,” inji Misis Angelica.
A wata tattaunawa da Misis Angelica ta yi da gidan Rediyon RCN Radio Barrankuilla ta ce, “Ta bar gida a shekarar 2018 bayan tsohon mijinta ya kore ta saboda wani sha’ani na danginsu da ya yi sanadin rabuwarsu.
Majiyar ta ce Misis Angelica ta bar gida kuma ba a samu rahoton inda ta shiga ba saboda tadade tana fama da rashin lafiyar kwakwalwa.
Misis Angelica ta bayyana wa kafafen labarai na Kwalombiya cewa ta fada tekun ne, bayan aka so ta ci gaba da rayuwa irin ta ’yan gudun hijira a yankin.
Wadanda suka ceto ta daga tekun sai da suka yi awa takwas a cikin ruwa kafin su fitar da ita daga ciki.