Mata 20 sun lashe zaben kansiloli a Saudiyya

A karon farko a tarihin kasar Saudiyya an zabi mata  20 a matsayin kansiloi bayan kammala zaben gundumomi da aka yi a kasar a karshen makon jiya.Hukumar zaben kasar ta bayyana Salma Bint Hizab al-Oteibi a matsayin daya daga cikin wadanda suka samu nasara, inda aka zabe ta kansila a majalisar yankin Makka. Bayan ta […]

Mata 20 sun lashe zaben kansiloli a Saudiyya
Mata 20 sun lashe zaben kansiloli a Saudiyya

A karon farko a tarihin kasar Saudiyya an zabi mata  20 a matsayin kansiloi bayan kammala zaben gundumomi da aka yi a kasar a karshen makon jiya.
Hukumar zaben kasar ta bayyana Salma Bint Hizab al-Oteibi a matsayin daya daga cikin wadanda suka samu nasara, inda aka zabe ta kansila a majalisar yankin Makka. Bayan ta samu kuri’u masu rinjaye kan abokan hamayyarta maza bakwai da wasu mata biyu.
Kusan mata dubu ne suka fito takara a wannan karo a kasar, da maza kusan dubu shida duk da cewar matan ba su da cikakken iko.
Zaben da aka gudanar a ranar Asabar shi ne karon farko da mata suka taka rawa a matsayin ’yan takara da kuma kada kuri’a.
A lokacin yakin neman zabe, ba a yarda mata su yi wa maza kamfen din nemansu kada musu kuri’a ba. Har ila yau, kamar yadda yake a dokar kasar ba a yarda mata su tuka kansu zuwa rumfunan zaben ba.  Hakazalika, an kebe rumfunan zabe na maza daban na mata daban lokacin zabubbukan.