Mata 30 Sun Samu Horo Kan Shirin Fim, Za Kuma A Nuna Shi A Kasashen Waje

Mata 30 ne a ka ba horo na musamman kan yadda a ke shirya fim a aikace a karkashin wasu kungiyoyin mata tare da tallafin ofishin jakadancin Faransa a Najeriya. A wani shiri na tallafawa mata na su tsaya da kafafuwansu a Kannywood. Horon wanda a ka gudanar a Kano, ya kunshi mata biyar da […]

Mata 30 Sun Samu Horo Kan Shirin Fim, Za Kuma A Nuna Shi A Kasashen Waje
hoto: Maikatanga
Mata na koyon daukar hoto a horon                        (Hoto: Girls Nation Academy/WIFIM)

Mata 30 ne a ka ba horo na musamman kan yadda a ke shirya fim a aikace a karkashin wasu kungiyoyin mata tare da tallafin ofishin jakadancin Faransa a Najeriya. A wani shiri na tallafawa mata na su tsaya da kafafuwansu a Kannywood.

Horon wanda a ka gudanar a Kano, ya kunshi mata biyar da aka zabo su daga kungiyoyin masu sana’ar shirya fina-finai da kuma wanda ke da alaka da aikin yada labarai.

  • https://aminiya.dailytrust.com/gani-ya-kori-ji-yadda-yan-kannywood-ke-atisayen-wasan-sarauniyar-zazzau
  • https://aminiya.dailytrust.com/hotuna-yadda-rarara-ya-raba-motoci-da-wayoyi-a-gasar-wakar-tinubu

A kuma gudanar da horon ne a zango na daya da na biyu a inda aka nunawa na tsawon kwanaki 4, an kuma nunawa matan yadda a ke shirya fim da kuma na’urorin da ake amfani da su, da kuma yadda ake amfani da na’urorin.

Wasu matan a karon farko sun rike kamara.            (Hoto: Girls Nation Academy/WIFIM)

A horon an koyar da matan matakan daukar fim tun daga kirkira, da tunani, da rubutawa, sannan ga daukar shirin yadda ya kamata, kuma a bisa tsarin da ake yi a duniya.

Banbancin Wannan Horon Da Sauran

Koyarwar an yi ta ne ta hanyar zamani tare da kayan aiki, a inda aka nuna musu na’urorin da ake aiki da su, da kuma yadda ake amfani da su din wajen Shirin fim.

A cewar Maryam Aliyu daga cikin mahalarta horon “an nuna mana yadda kamara ta ke aiki , sannan a ka kuma nuna mana yadda ake daukar hoto ya yi kyau”.

Karon farko mata na shrin daukar sauti a fim.         (Hoto: Girls Nation Academy/WIFIM)

Sannnan ta ci gaba da cewa, “An kuma nuna mana yadda ake daukar sauti, da haska fitila, da kuma yadda ake tace hoto. Wanda da a da sai dai su ga ana yi, duk da cewa muna fim”.

Daukar Nauyi

Kungiyoyin mata na kasa da kasa Girls Nation ne da kuma Women International film Makers WIFM ne, suka gudanar da horon, tare da tallafin ofishin jakadancin Faransa a Najeria.

Daya daga cikin jami’an da ke bayar da horon.    (Hoto: Girls Nation Academy/WIFIM)

Matan da a ka ba horon kuwa jarumai ne da ke fitowa a fina-finan Hausa, da marubuta, da masu shiryawa, daga kungiyoyin Arewa Film Makers Association, MOPPAN da sauran wasu kungiyoyi masu zaman kansu da ke ciki da wajen Kano.

Fa’idar Horon

A sakamakon wannan horo a cewar Salisu Mohammed na kungiyar Arewa Film Makers, “yanzu za a samu mata masu sana’ar daukar hoto, da daukar sauti, da sauran wasu sana’oin da maza ne kadai ke yin su a Kannywood, wannan kuma ba karamin cigaba ba ne”.

Matan da aka ba horon tare da malamansu. (Hoto: Girls Nation Academy/WIFIM)

Fatan da ake yi shine da hakan masana’antar Kannywood za ta farfado tare da kara saninta a duniya, sakamakon shirin nuna fim din da matan 30 din su kayi, a bikin nuna fina-finai na duniya, idan an gama daukarsa a nan.