Mata 4 da ’ya’yansu sun tsere daga hannun ’yan bindiga a Katsina

Sojoji sun gano mutanen suna yawo a daji bayan sun tsere daga hannun ’yan bindiga.

Mata 4 da ’ya’yansu sun tsere daga hannun ’yan bindiga a Katsina

Wasu mutane shida sun yi nasarar tserewa daga hannun ’yan bindiga a yankin Karamar Hukumar Faskari ta Jihar Katsina.

Birget na 17 na Rundunar Sojojin Najeriya ta sanar cewa dakarunta sun samu nasarar ceto mutanen, mata hudu da yara biyu.

Rundunar ta ce yayin sintirin ƙafa a yankin Unguwar Doka a ranar 29 ga Yuni ne sojojin suka gano mutanen suna yawo a daji bayan sun tsere daga hannun ’yan bindiga.

Sanarwar da kakakin rundunar, Kyaftin Abayomi Adisa ya fitar a ranar Talata, ta ce binciken farko ya nuna cewa ’yan bindiga ne suka yi garkuwa da su mutanen daga Unguwan Lado a Karamar Hukumar Kankara tun ranar 22 ga watan Yuni.

Sojojin sun ba su taimakon gaggawa, sun ci abinci tare da samun kayan bukata kafin a mayar da su ga iyalansu.

Kwamandan Birget na 17, Birgediya Ishaya Ibrahim, ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da kai hare-hare kan ’yan ta’adda da sauran miyagu domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Ya kuma kara da cewa rundunar sojojin Najeriya za ta kara kaimi wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a fadin Jihar Katsina.