Mata 5200 sun samu tallafin jari
Kimanin mata 5,200 ne suka samu tallafin Naira dubu goma-goma da a matsayin jarin da za su fara sana’o’in da suka sami horo akai. Tallafin jari na Naira dubu 10 wanda Gwamnatin Jihar Kano ta raba wa matan an raba shi ne a karshen makon da ya gabata. Kwamishinan harkokin mata ta Jihar Kano Hajiya. […]
Kimanin mata 5,200 ne suka samu tallafin Naira dubu goma-goma da a matsayin jarin da za su fara sana’o’in da suka sami horo akai. Tallafin jari na Naira dubu 10 wanda Gwamnatin Jihar Kano ta raba wa matan an raba shi ne a karshen makon da ya gabata. Kwamishinan harkokin mata ta Jihar Kano Hajiya.
’Yardada Maikano Bichi ta bayyana cewa shirin ya samo asali ne a kokarin da gwamnatin Kano don ganin an tallafa wa mata sun tsaya da kafafuwansu. Yardada ta yi kira ga matan da suka amfana da su yi amfani da tallafin da ka ba su wajen yin sana’oin da suka koya.
“Mmuna kira ga mata da su yi amfani da kudin wajne yin sana’a ko fadada sanaarsu ba wai su je su sayi atamfa ko kayan daki da kudin ba. Muna fatan za su juya su don su karu su zama wani abu don tallafawa iyalansu.”
Da yake raba kudin tallafin ga matan da suka sami tallafin Gwamann Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa gwamnatinsa ta yi hakan ne don tallafa wa mata yadda za a samu rayuwar iyali ta inganta.
“Muna sane da yadda mata ke tsaye akan iyalansu don haka muke so mu kara musu karfin gwiwa ta hanyar ba su tallafi yadda za su inganta sana’o’insu tare da taimaka wa rayuwar iyalansu”
Gwaman Ganduje ya bayyana cewa za su sama wa matan kasuwa ta musamman wacce za a rika hada-hadar kayan da aka kera a gida Kano.
Haka kuma ya yi wa matan albishir cewa gwamnatin ta ware Naira miliyan 50 don sayen kayayyakin da matan suka sarrafa don raba wa ga ‘yan gudun hijira da ke Arewa maso gabashin kasar nan. “
Hajiya Aisha Sani Abubakar Shugabar Mata ce a rukunin gidaje na danladi Nasidi tana daya daga cikin matan da suka samu wannan tallafi ta yi godiya- game da horon da kuma tallafin da ta ba su
“Na koyi sabulu da kayan gyaran jiki zan kuma yi amfani da wanan kudi wajen yin jari na sana’ar da na koya. Allah ya saka wa gwamantin Ganduje da alheri”
Ita ma Malama Maryam Maidanwake a karamar Hukmar Kumbotso ta bayyan cewa tallafin zai taimaka mata kwarai da gaske wajen yin sana’arta tare da kula da marayun ‘ya’yanta.