Mata a nemi ilimin aure kafin yinsa

Godiya ta tabbata ga Allah (SWT) wanda Ya halicci komai. Babu wani abu mai faruwa ba tare da nufi da ikonSa ba. Tsira da aminci su tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW) da Alayensa da Sahabbansa da wadanda suka biyo bayansu da kyautatawa, har ya zuwa ranar tashin Alkiyama. Manufar wannan mukalar don mata […]

Mata a nemi ilimin aure kafin yinsa
Mata a nemi ilimin aure kafin yinsa

Godiya ta tabbata ga Allah (SWT) wanda Ya halicci komai. Babu wani abu mai faruwa ba tare da nufi da ikonSa ba. Tsira da aminci su tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW) da Alayensa da Sahabbansa da wadanda suka biyo bayansu da kyautatawa, har ya zuwa ranar tashin Alkiyama. Manufar wannan mukalar don mata sun san ilimin aure kafin su yi shi ne, amma saboda abokan zamansu maza zan jagoranci mukalar a kan maza da mata, don bai kamata a doki jaki a bar taiki ba.
Bai halarta ga wani ya yi aure ba, har sai ya san hukuncinsa. A yanzu bai zama abin mamaki ba komai na Musulmi na nan kara zube, babu sanin hukuncin Islama, babu ilimin sauke farillan da suke kansu, idan haka ne ta ya ya za su dora wa kansu hakkin waninsu, alhali sallah ba su karanta yadda ake yinta ba, wai kuma ana tsammanin su bayar da tarbiyya tagari.
A yanzu kowa na kokari wajen neman ilimin rayuwar duniya, amma sha’anin rayuwar da ta hada da Allah ana yinta ne da ka. Don haka wajibi ne mata da maza da suka doshi yin aure su karanci hukuncin aure da dukkan ilimin da ya shafi auren a cikin addinin musulunci, domin ba ya halarta a aikata aiki sai an san hukuncinsa cikin addini. Ya zo cikin sharhin Ibn Majah “Abubuwa da yawa ba wajibi ne mutum ya yi iliminsu ba, amma ba ya halatta kuma ka aikata wani abu sai kana da iliminsa”. Misali- ba wajibi ba ne kowa ya san ilimin kasuwanci, amma ba ya halatta ga Musulmi ya fara kasuwanci sai ya yi iliminsa, haka ma aure iliminsa ba ya zama wajibi a kan kowa, amma duk wanda ya yi nufin aure, ba ya halatta ya yi sai ya san hukuncinsa a cikin musulunci, kamar sanin ilimin aure, hakkin miji da mata, nauyin ilimi da rayuwar matansa da ibadarsu da sauransu. To mai za ku ce ga wadanda suka yi aure ba su iya ko da Ahlari ba? A yanzu daga mutum ya yi wayo zai rika kokari wajen karatun zamani don neman duniya. Don haka ‘yan uwana mu yi kokari wajen neman yadda za mu sauke nauyin da ke kanmu. Allah Ya sa mu dace, amin.
  AURE: Ibada ne daga Allah (SWT), kuma ana yi ne don neman rahamarSa da yardarSa, in haka ne to ku sani yin aure kawai don al’ada ko rashin niyyar ibada, ba ya daga cikin sakamako wajen Allah. Don Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Duk wani mutum da niyyarsa ake saka masa a cikinsa” (Bukhari da Musim, hadisin Umar dan Khattab).
Don haka za a fahimci cewar aure dai sunna ne mai karfi daga cikin sunnonin Manzon Allah (SAW), kamar yadda ayoyi da dama suka nuna mana, Allah Yana cewa: “Hakika mun aiko manzanni (da yawa) kafin ka zo (ya Muhammad (SAW) kuma muka sanya a gare su, mataye (da yawa) da zuriya…..” (Ra’adi 38). A wata ayar kuma ya ce: “Yana daga ayoyinsa (Allah) Ya halitta muku matayenku daga gare ku (maza da mata), domin ku natsu izuwa gare su, kuma ya sanya kauna da tausayi a tsakaninku, lallai cikin wannan akwai ayoyin (lura) ga mutane masu tunani.” (Rum 21).
A wata ayar kuma umarni Ya bayar: “Ku auri abin da ya yi muku dadi daga mata, bibbiyu, uku-uku ko hur-hudu, to amma idan kun ji tsoron ba za ku yi adalci ba (a tsakanin mata fiye da biyu!) to ku (auri) daya tak,……” (Nisa’i aya ta 3).
Saboda muhimmancin aure ne ma ya sa Manzon Allah (SAW) ya hana wasu sahabbai su fidiye kansu, kamar yadda Sa’ad bin Abi wakkas (RA) ya yi bayani. (Bukhari 1467). Kuma Manzon Allah (SAW) ya nuna aure sunnarsa ce: “Duk wanda ya kyamaci sunnata, to ba ya tare da ni” (Bukhari 5063, Muslim 1401).
   Don haka aure sunna ce, kuma duk wani mai daraja ta wannan hanyar yake kare mutuncinsa.
Za mu ci gaba

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya