Mata a nemi ilmi don tallafa wa mazaje – Uwargidan Gwamnan Kebbi

Uwargidan Gwamnan Jihar Kebbi, Hajiya A’isha Sanata Abubakar Atiku Bagudu ta shawarci mata su tashi tsaye wajen neman ilimi, domin taimaka wa mazansu, kuma su samar da kyakkyawar tarbiyya ga ’ya’yansu. Kakakin matar Gwamnan, Na’omi Zuru ce ta bayyana haka a lokacin da take zantawa da wakilinmu a Birnin-Kebbi.Matar Gwamnan ta yi nuni da cewa, […]

Mata a nemi ilmi don tallafa wa mazaje – Uwargidan Gwamnan Kebbi
Mata a nemi ilmi don tallafa wa mazaje – Uwargidan Gwamnan Kebbi

Uwargidan Gwamnan Jihar Kebbi, Hajiya A’isha Sanata Abubakar Atiku Bagudu ta shawarci mata su tashi tsaye wajen neman ilimi, domin taimaka wa mazansu, kuma su samar da kyakkyawar tarbiyya ga ’ya’yansu.

Kakakin matar Gwamnan, Na’omi Zuru ce ta bayyana haka a lokacin da take zantawa da wakilinmu a Birnin-Kebbi.
Matar Gwamnan ta yi nuni da cewa, ‘lokaci ya wuce da mata za su zura wa mazansu ido, musamman a wannan lokaci da ake ciki na rashin kudi.
Uwargidan gwamnan ta kuma bukaci mata su hada kai da mazansu don samun gagarumar nasara a harkokinsu na rayuwa.
Sai ta shawarci iyaye maza su kasance masu kula da tar biyyar ’ya’yansu, tare da sanya su a makaranta, ta yadda za su kaurace wa shiga cikin miyagun halaye da za su sanya iyaye cikin halin kaka-nika yi. Hajiya Aishatu Atiku Bagudu ta yi nuni game da irin rawar da mata ke takawa wajen tarbiyyaar da iyali, inda ta ce amma hakan ba zai samu nasara sai da hadin kan maza a matsayinsu na jagororin iyali.
Tta yi kira ga mata masu ilimin zamani su rika karantar fannin aikin asibiti, domin taimaka wa ’yan uwansu mata, musamman a fannin haihuwa da sauran cututtukan da suke addabar mata, maimakon a ce maza likitoci ne ke duba wadanda ba muharramansu, ba.
Ta ce duk inda ake da gibi a bangaren kiwon lafiya za su yi kokarin taimaka wa mata wajen karatun aikin lafiya.