Mata a rike gaskiya

Hajiya Umma Hassan Wayo ita ce Shugabar kungiyar Masu Keke Napep ta Jihar Filato, har ila yau  ita ce shugabar kungiyar nan mai tallafawa mata ta Hikima da ke garin Jos. A wannan tattaunawa da ta yi da wakilinmu ta bayyana irin gwagwarmayar da ta sha musamman wajen tallafawa mata da matasa.  Ga tattaunawar kamar […]

Mata a rike gaskiya
Mata a rike gaskiya

Hajiya Umma Hassan Wayo ita ce Shugabar kungiyar Masu Keke Napep ta Jihar Filato, har ila yau  ita ce shugabar kungiyar nan mai tallafawa mata ta Hikima da ke garin Jos. A wannan tattaunawa da ta yi da wakilinmu ta bayyana irin gwagwarmayar da ta sha musamman wajen tallafawa mata da matasa.  Ga tattaunawar kamar haka:

Tarihin rayuwata;
Sunana Hajiya Umma Hassan Wayo.   An haife ni a garin Jos.   Na yi makarantar firamare a Jos, kuma na fara makarantar sakandire ta GSS Jos  daga nan na koma Kano. Na kammala  sakandare  a Jogana. Daga nan sai mahaifina ya ce ya dace ya yi mani aure, don haka daga nan aka yi mini aure.

Aiki na;
To,  ni ‘yar kasuwa ce domin tun ina gidan mijina na farko na soma harkokin kasuwanci. Na kan je Kano na sayo kaya na kawo na raba wa mutane a nan Jos, har Allah Ya daukaka wannan harkokin kasuwanci inda ya kai har ina fita zuwa kasashen waje na sayo kaya na zo na rabar a nan Jos. Kuma ni ‘yar siyasa ce.

kungiyoyin da nake ciki:
Ina cikin kungiyoyi da dama domin  ni ce shugabar kungiyar tallafawa mata ta Hikima Women Debelopment Association da ke garin Jos. Wannan kungiya ce ta tallafawa mata kuma mun fara ta ne da mata  10  amma a yanzu muna da mata 150 kuma muna tara kudi ne a tsakaninmu mu rabawa mata na kasa da mu bashi ba tare da ruwa ba, domin su je su yi sana’o’i. Da farko mun fara da tara Naira dubu 25 a duk wata muna rabawa mata bashi amma a yanzu ya kai a duk wata muna tara Naira  miliyan 12 muna rabawa mata bashi ba tare da ruwa ba. Haka kuma ni ce shugabar bunkasa zaman lafiya a tsakanin matasa da mata  a Jihar Filato da Nijeriya baki daya.   Kuma ni ce shugabar kungiyar  masu Keke Napep ta Jihar Filato. Kuma ina cikin kungiyar nan da take wayar da kan al’ummar  mata Hausa/Fulani kan harkokin siyasa a  karamar hukumar Jos ta Arewa.

Nasarorin da na samu:
Babu shakka akwai nasarori, domin kamar yadda na fada  a kungiyarmu ta  tallafawa mata ta Hikima Debelopment Association,  mun fara da tara  Naira dubu 25 a duk wata  amma a yanzu a duk wata muna tara  sama da Naira miliyan 12, muna rabawa mata bashi ba tare da ruwa ba, don su yi jari kan sana’o’in da suke yi. Haka kuma a kungiyar masu Keke Napep ta Jihar Filato nan ma na samu nasarori da dama. Domin  na fara ne da sayen babura ina rabawa matasa bashi, na fara  da sayen babura guda 6 amma kafin a hana sana’ar acaba a nan garin Jos da kewaye ina da babura guda  60.  Daga nan muka fara wannan sana’a ta Keke Napep bayan da aka hana sana’ar acaba.  A yanzu a duk jihar Filato, babu wanda yake da yawan Keke Napep kamar ni. Domin a yanzu ina da Keke Napep sama da guda 300. Don haka  a takaice ina ganin na samu nasarar   samarwa mata da  matasa sama da dubu  ayyukan yi.

kalubale:
Duk abin da za ka yi a rayuwa dole sai ka samu kalubale don haka na samu kalubale da dama a wadannan abubuwa da nake yi. Musamman a wannan
kungiya ta tallafawa mata ta Hikima, wasu sukan ce yankan kai muke yi, wasu kuwa ce wa suke y maza ne suke ba mu kudin da muke tarawa, wasu suna cewa mune a tsakaninmu  muke neman junanmu muke samun wadannan kudi. Mun je har gaban malamai a Jos mun gaya masu abubuwan da muke yi tare da kudurorinmu kuma sun gamsu. Abin da na so na yi lokacin da nake karama. 

A gaskiya lokacin da nake karama saboda gidanmu gidan karatu ne, na so na zama likita ne domin a gidanmu muna da wadanda suka yi digiri kusan mutum 20.   Muna da wadanda suka yi digiri na biyu  mutum 5 amma sai ya zama daga kaina Babanmu ya dakatar da cigaba da karatun Jami’a a gidanmu. A lokacin na yi kuka na tambayi mahaifinmu dalilinsa  kan wannan mataki da ya dauka sai ya ce mini wannan shi ne ra’ayin da ya dauka.

kasashen da na ziyarta:
Na je kasar  China sau daya.   Na je Dubai sau biyar.   Na je Saudiyya sau tara sannan na je Kenya sau uku.

Iyali:
Ina da yara uku da mijina na farko. Bayan na sake wani auren wanda muke tare da shi a halin yanzu Allah ya azurtamu da yarinya daya. A takaice dai ina da yara hudu maza biyu mata biyu,  yanzu haka babban dana  yana da shekaru 16, zancen da nake yi maka yanzu haka yana Abuja don shirye shiryen tafiya kasar Uganda don  ya yi karatun digiri a can.

 Yadda nake hada harkokina da kula da iyali:
 Ina baiwa mijina da ‘ya’yana  lokacin su  domin kamar yau din nan ma mijina  ya gaya mini cewa yana son nayi masa miya kafin na fita. Haka na tsaya  na yi masa  kafin na fita.

Tufafin da nafi so:
Ni ko teloli na sun  cewa ina son dinki ne na mutumci wato ina son tufafi wadanda zasu tsare mani mutumcina tare da mijina da ‘yayana.

Abincin da nafi so:
A gaskiya nafi sha’awar tuwo da miyar kuka Abin da nake son a rika tunawa da ni ko bayan raina

Abin da na fi so a rika tunawa da ni:
Ina son a rika tunawa da ni kan ayyukan alherin da na yi

Shawarata ga mata:
Shawara ta ga mata ita ce mata a rike gaskiya da amana   domin duk macen da aka ce ta rike gaskiya da amana ta zama abokiyar zama. Duk
mutumin da ya samu mace mai gaskiya da rikon amana,  ya rufe kofa. Don haka ina shawartar mata su rike gaskiya da amana idan suka yi haka, za su ji dadin rayuwarsu a nan duniya da gobe kiyama.