Mata A Yau: Mai gabatarwa ta magantu kan batun gaishe da miji

Binta Suleiman ta bayyana wanda ke gaida wani tsakanin miji da mata a gidansu

Mata A Yau: Mai gabatarwa ta magantu kan batun gaishe da miji

Daya daga cikin masu gabatar da shirin Mata A Yau da ya jawo ce-ce-ku-ce kan wanda kamata ya gaishe da wani tsakanin mata da miji ta magantu a kan batu.

Binta Suleiman Gaya, ta yi tsokacin ne bayan suka da tatkwarorinta masu gabatar da shirin suka sha, da kuma zargin su neman lalata zamantakewar aure ta hanyar tallata abin da ya ci karo da koyarwar Musulunci da koya wa mata rashin da’a.

Dambarwar ta taso ne a shirin na Mata A Yau na tashar Arewa24, bayan daya daga cikin masu gabatarwa, Aisha Umar Jajere, ta ambato wani magidanci da ke son rabuwa da matarsa saboda ba ta gaishe, inda mai gabatarwar ta kada baki ta ce, “idan ba ta gaishe ka ba, to ai kai sai ya gaishe ta.”

Hakan dai ya faru ne a lokacin da Binta, wadda malamar jami’a ce, ba ta cikin shirin, kuma furucin A’isha Jajere ya sa mutane musamman malaman Musulunci suka yi ca a kan shirin da ma masu gabatarwar.

A yayin da kurar ta fara lafawa ne a ranar Juma’ar nan, Binta Suleiman Gaya, ta yi tsokaci a shafinta na Facebook, cewa ita a tarbiyyar gidansu mace ke gaida mijinta, sannan ta siffanta yadda gaisuwar take.

“A gidanmu, na taso maigida ke zagaya wa yana duba lafiyar iyalinsa shi duk safiyar Allah.

Mu kuma da mun gan shi sai mu tsuguna mu gaishe shi ‘ranka ya dade’ ko barka da asuba, ba ma mikewa har sai ya yi mana sallama ya fita,” in ji ta.

Ta ci gaba da cewa, “Mu muna daga bangaren ayar Al-Kur’anin nan da ta ce miji shi ne shugaba a gidansa (Nisa’i:34), shi kuma na san sunnar Manzon Allah (saw) yake bi. Wannan itace tarbiyyar da akai mana tun muna yara, kuma ita ce muke rike da ita.”

Ta kara da abin da ake ganin caccakar abokan aikin nata ne da yi wa batutuwa dibar karan mahaukaciya, inda ta ce, “Nema wa mata mafita ba kara zube ake yi ba, ba ’yancin fitsara ake nema ba, hanya ake nema ta hada kai da ci gaban al’umma, yaye talauci, da tarbiyyar yaranmu gaba daya; duk rayuwar da babu shugaba ba zata taba daidaituwa ba.”

Idan za a iya tunawa caccakar da malama suka yi wa masu gabatar, ta sa suka dangana da ofishin shugaban hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya sa baki.

Bayan ganawa da matan, Sheikh Daurawa ya bayyana cewa sun nuna damuwarsu kuma sun ba da hakuri bisa abin da ya faru, kuma ba a fahimce su ba ne.

Sun bayyana cewa kuskure aka samu, amma ba abinda suke son isarwa ba kenan, inda suka bayyana cewa hankalinsu ya tashi sosai kan yadda jama’a suka taso mu su.

Yadda gwamnati ta yi sulhu da ’yan bindigar Kaduna

‘Da kuɗin yankan farce na je Hajji’

Zambar Intanet: EFCC ta kama ’yan China 4 da wasu 101 a Abuja

Gwamnan Akwa Ibom ya kori duk Kwamishinoninsa