Mata ba daidai suke da maza ba- Shugaba Erdogan
Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce mata ba daidai suke da maza ba, inda ya bukaci a daina daukar mata kamar maza.Ya bukaci masu rajin kwato wa mata ’yanci su fahimci babban abin da mata za su yi shi ne lura da iyali ba wai gogayya da maza a wurin aiki ba.Ya ce […]
Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce mata ba daidai suke da maza ba, inda ya bukaci a daina daukar mata kamar maza.
Ya bukaci masu rajin kwato wa mata ’yanci su fahimci babban abin da mata za su yi shi ne lura da iyali ba wai gogayya da maza a wurin aiki ba.
Ya ce “Ba za ka taba sanya mata da maza a kan faifai daya ba, saboda halittarsu ba daya ba ce.” Ya ce haka yayin wani taro a Istanbul da ke Turkiyya a ranar Lahadi.
Ya ce masu rajin kare hakkin mata ba su fahimci darajar mata a Musulunci ba.
Wakilin BBC Mark Lowen ya ce kalaman Erdogan ya haifar da cece-kuce a kasar, inda masu adawa da shi suka rika amfanin da kalamansa wajen kamfe.
Erdogan ya bukaci mata su rika haihuwar ’ya’ya 3, sannan ya yi kira a daina zubar da ciki ko haihuwa ta hanyar tiyatar caesarean.
A lokacin wani taron da ya shafi mata a Turkiyya ya ce ba za a taba kwatanta halittar mata da ta maza ba.
“A wurin aiki ba za ka taba ba namiji aiki iri daya da mace mai ciki ba. Mata ba za su iya dukkan ayyukan da maza za su yi ba, saboda yanayin jikinsu ba daidai yake da maza ba. Addininmu ya daraja mata, ya daukaka su, don haka masu rajin kare hakkin mata su fahimci kariyar da addinmu ya ba su.”
Ya kamata a daraja mata ne ba wai a ce darajarsu daya da ta maza ba.
Erdogan ya ce adalci shi ne abin da zai magance wariyar launin fata da matsalolin da mata suke fuskanta.