Mata da cututtukan zamani (1)
A ci gaba da nazari da muke yi a kan mata da cututtukan zamani a wanannn mako za mu dubu yadda jahilci da kunya ke sanyawa mafi yawan mata suke fadawa cikin tarkon kamuwa da cututtuka masu yawa a wannan zamanin da muke ciki.Da dama daga matanmu sun jahilci yadda ake kamuwa da irin wadannan […]
A ci gaba da nazari da muke yi a kan mata da cututtukan zamani a wanannn mako za mu dubu yadda jahilci da kunya ke sanyawa mafi yawan mata suke fadawa cikin tarkon kamuwa da cututtuka masu yawa a wannan zamanin da muke ciki.
Da dama daga matanmu sun jahilci yadda ake kamuwa da irin wadannan cututtuka, kamar cutar sanyi irin su gonoriya da tsargiya da yankan gashi da sauransu, wadanda suke haddasa kaikayin gaba da kuraje da fitar ruwa daga gaban mace ko namiji da wari farjin mace da sabar azzakari da kankacewar azzakari da kumburin farji da azzakari da sauran su.
Babu shakka mafi yawan mata sun kamu da irin wadannan cututtuka, amma sai kunya ta hana su bayyanawa don a nema musu magani. Idan matar aure ce sai ka ga ta boye wa mjinta don jin tsoron kada ya zarge ta da fasikanci, idan kuwa budurwa ce sai ita ma ta boye wa saurayin da zai aure ta saboda tsoron sakamakon abin da zai haifar.
Ba komai ke janyo wa mata suke boye kamuwa da cututtukan ba sai tsabar jahilci, domin idan da sun san hadarin barin cutar a jikin dan Adam da sun yi gaggawar bayyanawa domin a gaggauta nema musu magani. Wani abin mamaki shi ne za ka ga yarinya budurwa tana fama da irin wadannan cututtuka, amma sai ka ga ta boye wa mahaifiyarta duk da irin shakuwar da suka yi. Haka za a yi mata aure ba tare da sanin iyayenta ba ko saurayin da ya aure ta, sai daga bisani idan mijin ya kamu a rika kame-kamen yadda za a yi maganin abin.
Wata kuwa saboda tsabar jahilci sai ta rika bin kawayenta tana gaya musu tana tsammanin za su taimaka mata, amma daga bisani sai su ci amanarta su rika yada ta a duniya har ya kai idan wani saurayi ya fito zai aure ta su gaya masa cewa tana da ciwon sanyi. Shi ya sa shawarar da nake bai wa mata ita ce duk lokacin da suka fahimci sun kamu da daya daga cikin wadannan cututtuka, to su natsu, kada su tayar da hankalinsu, su tafi asibiti kai tsaye a auna su a tabbatar da irin dangin ciwon sanyin da yake damun su, ta yadda za a san maganin da za a ba su. Wannan shi zai sanya su ma su san irin nau’in cutar sanyin da take damun su.
Wani abin lura shi ne babban dalilin da ya sa wasu matan suke boye cutar shi ne gudun tsangwama daga wadanda ke tare da su, kamar iyaye da ’yan’uwa. Don mafi yawan jama’armu idan aka yi zancen ciwon sanyi abin da suke fara tunani shi ne, mutum ya dauka ne ta hanyar banza kamar jima’i.
Saboda haka ya kamata jama’a su daina rudewa don sun kamu da wata cuta, abin da ya kamata mutum ya yi shi ne, ya tafi asibiti a auna shi, a tattabar da nau’in cutar, kuma ya nemi maganin bature, idan na bature bai karbe shi ba, to ya gwada na musulunci ko na gargajiya. Da yardar Allah zai samu lafiya.
Amma kuma ya kamata mutane su rika kiyaye hanyoyin da ake daukar wadannan cututtuka kuma su tsare kansu da iyalensu sannan kuma a guji jita-jita.
Abubakar Haruna ya rubuto daga Legas 08027406827 [email protected].