Mata da kafafen sadarwa: Kada a zunguro sama da kara

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili mai albarka. Muna fata kuna cikin koshin lafiya. A wannan makon mun yi muku guzurin bayani ne kan yadda kafafen sadarwa suke dauke hankalin mata har su manta da ayyuka masu muhimmancin da ke kansu. Muna fata wannan matashiya za ta kasance sanadiyyar da mata za […]

Mata da kafafen sadarwa: Kada a zunguro sama da kara
Mata da kafafen sadarwa: Kada a zunguro sama da kara

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili mai albarka. Muna fata kuna cikin koshin lafiya. A wannan makon mun yi muku guzurin bayani ne kan yadda kafafen sadarwa suke dauke hankalin mata har su manta da ayyuka masu muhimmancin da ke kansu. Muna fata wannan matashiya za ta kasance sanadiyyar da mata za su fito daga duguwar ninkayar da suka yi wajen amfani da kafafen sadarwa na zamani. Allah Ya sa bayanin ya amfanar da wadanda aka yi domin su, amin.

Matashiya:
A ranar Litinin ne Babban Hafsan Hafsoshin Najeriya Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya kawo ziyara fadar Gbong Gwom Jos, Da Jacob Buba Gyang, hakan ya sa aka gayyaci ’yan jarida don su rawaito wainar da za a toya, a cikin wadanda aka gayyata kuwa har da ni a ciki. Bayan ya gana da Gbong Gwom Jos ne, muka wuce zuwa karamar Hukumar Shendam da shi, inda ya ziyarci rundunar sojojin da ke karkashin Babbar Rundanar Sojojin Najeriya ta 3, a yayin ziyarar tasa ya gana da wadannan sojoji, sannan ya yi musu jawabin karfafa gwiwa. A takaice ba mu samu dawowa Jos ba sai da misalin karfe 7:00 na dare, daf da za mu iso garin Jos ne na ji wani abokina wanda shi ma dan jarida ne ya kira matarsa, inda yake sanar da ita mun kusa karaso wa Jos, sannan ya tambaye ta ko ta kammala dafa abincin dare? Yadda ya ci gaba da magana ne ya nuna mini abincin yana kan wuta, kasancewar ya ce mata ta yi sauri ta gama.
Bayan ya ajiye wayar sai ya kalle ni, sannan ya ce, “Kado, yau fa a gidana za ka ci abincin dare.” Na kalle shi cike da mamaki, “Me ya sa ka ce haka?” Na tambaye shi bayan na gyara zamana. Bayan ya fuskance ni sosai, “Abincin da ka fi so ake girkawa a gida.” Ya ce da ni yana murmushi. Ni ma na yi murmushi. Abokaina sun san babu abincin da na fi so kamar tuwon shinkafa da miyar taushe mai dauke da kayan ciki, sannan a zuba mata man shanu da yajin daddawa. Ganin na ci gaba da kallonsa ban ce komai ba, sai ya ce, “Na san ba ka isa ka ce ba za ka zo ba, akwai man shanu da kayan ciki har da yajin daddawa.” Ya fashe da dariya, take na ji yawun bakina ya tsinke, amma duk da hakan bai hana ni yin dariya ba.
“Kada ka damu, yau a gidanka zan ci abincin daren.” Na tashe da shi cikin jin dadi duk da cewa gajiyar da muka yi ta ci karfi na. Ya fashe da dariya, “Ai dama na san ba ka isa ka ki amsa gayyata ba.Janke, har kwadayinka ya tashi.” Ya ce da ni bayan ya daina dariyar.
Bayan sojojin sun ajiye mu a sakatariyar ’yan jarida ta Najeriya (NUJ) reshen Jihar Filato ne sai muka karasa wurin da na yi wa motata matsugunni, sannan na bude muka shiga sai gidansa. har muka isa gidansa muna hirar yadda Laftanar Janar Buratai yake dawowa da martabar sojojin Najeriya.
Yanayin yadda na ga matarsa bayan mun shiga gidan ne ya nuna mini akwai wani abu a kasa, domin gaba daya hankalinta a tashe yake. Mun gaisa da ita, amma hankalinta ba ya kaina, inda a lokutan baya wani lokaci har zolayata take yi. Daga nan ta ce wa abokina tana son magana da shi. Suka shiga daki suka bar ni a falo inda na zuba wa talabijin ido, fim din Indiya mai suna ‘Solana’ take kallo lokacin da muka shigo falon.
Bayan wani lokaci ne na ga ya fito daga dakin yana huci kamar kububuwa, daga baya ne ya sanar da ni cewa wata hira da take yi a wani guruf na Whatsapp ne ya dauke mata hankali har miyar ta kone, tuwon ma ya kone. Abin ya ba ni mamaki, ban ce komai ba, saboda ba zan shiga tsakanin mata da miji ba. Daga baya ne yake shaida mini ba wannan ne lokaci na farko da hakan ke faruwa ba, hankalinta kan gushe a lokacin da take latse-latsen waya bayan ta shiga shafukan kafafen sadarwa na zamani. Kwadaiyana ya koma, murnata ta koma ciki, haka dai aka dafa mana indomie muka ci, amma dai zuciyata na kan tuwon shinkafa miyar taushe.
A lokacin da muke cin Indomie ne ya bukaci in yi rubutu a kan abin da ya shafi matan da ke tu’ammali da kafafen sadarwa na zamani har su rika mantawa da muhimamman ayyukan da suka wajaba a kansu.
Tun da ya ba ni labarin abin da ya faru na ji al’amarin ya kara tsayawa a raina, kasancewar ba wannan ne lokaci na farko da na taba cin karo da batu irin wannan ba. Hakan ya sanya na kuduri aniyar yin wannan rubutu don ganin na fadakar da mata illar da ke tattare da mayar da hankalin kan wadannan kafafen sadarwar na zamani kocakon har su rika mantawa da muhimman ayyukan da suka wajaba a gare su.
A makon gobe insha Allah zan zo da cikaWkken bayanin kan hadarin da wadannan kafafen sadarwa na zamani suke da shi ga matan da suka mayar da hankalinsu gare su.
Za mu ci gaba inshaAllah.