Mata da kalubalen rubuce-rubucen jiya da yau

Mata da dama a tarihi, sun zama manyan malamai masu ilimantarwa a cikin al’ummarsu, musamman ’yan uwansu mata. Kamar yadda aka samu, a tarihi, sun zama manyan shugabanni masu iya tafiyar da mulki a cikin hikima da ilimi, wadanda har ma shawarar maza ba ta iya zarta ra’ayinsu da tunaninsu. Misali sarauniya Bilkisu, wacce mace […]

Mata da kalubalen rubuce-rubucen jiya da yau
Mata da kalubalen rubuce-rubucen jiya da yau

Mata da dama a tarihi, sun zama manyan malamai masu ilimantarwa a cikin al’ummarsu, musamman ’yan uwansu mata. Kamar yadda aka samu, a tarihi, sun zama manyan shugabanni masu iya tafiyar da mulki a cikin hikima da ilimi, wadanda har ma shawarar maza ba ta iya zarta ra’ayinsu da tunaninsu.

Misali sarauniya Bilkisu, wacce mace ce mai matukar hikima da ilimi. Daga cikin matan da suka ba da gudunmawa ta  wannan  fuskar, akwai daya daga cikin ’ya’yan Shehu Usman dan Fodiyo  wato Nana Asma’u, wadda ita aka fi sani, wajen ba da gagarumar gudunmawa ga ’yan uwanta mata. Duk da karancin shekarunta, amma hakan bai hana ta bin tafarkin mahaifinta ba, na ba da ilimi da kuma hidimomi ga yaduwarsa.

Nana Asma’u ta kafa kungiyar mata masana, ta kasance gogaggiyar malama ce wacce yara da mata ke koyon karatu a karkashinta.Ta ce niyya na da muhimmanci, ni kuma ina koyar da su addinin Allah (ne) don in sauya su daga mugun nufi in dura musu ilimin da ya wajabta a kansu, kamar su alwala da Sallah da Azumi da Zakka da Hajji, wadanda suka wajaba a kan baligi (ya sani).

Nana Asma’u ta yi aiki tukuru wajen rubuta fannoni daban-daban na gwagwarmayar Shehu dan Fodiyo.   Haka ta shafe rayuwarta tana wannan namijin aikin na ilimantar da mata. Hakika ta zama tushe na har abada wajen karfafawa ga mata Musulmi na yau.

Haka akwai yayar Nana Asma’u mai suna Khadija, wacce malama ce marubuciya mai koyarwa. Ta rika rubuta wake-wake na hobbasa ga ’yan uwanta mata da hukunce-hukuncen Musulunci, kuma kwararriyar malamar mata ce a hubbare.

Cikin matan da suka ba da gudunmawa, akwai Amina Haidar Assadar, wacce aka fi sani da Bintul Jihad. A rubuce-rubucenta ta kawo wata kungiya a gidan mijinta Wazirin Sakkwato, kungiyar ta hada da matan da suke zuwa daga nesa da kusa don koyon Alkur’ani da hukunce-hukuncen addini da wasu bangarori na Musulunci don su koma gidjensu su karantar da ’yan uwansu mata.

Yanzu haka wannan makaranta tana nan gidan Wazirin Sakkwato, ana ci gaba da koyar da matan birni da kauye wadanda suke zuwa musamman don neman ilimi. Akwai inda ta bayyana a wakenta na gwagwarmayar neman ilimin mata kamar haka:  A yayin da zafi da bazara lokacin da iska mai zafi take kadawa; da farkon lokacin fara ruwa, Hauwa na bisa hanya tana kawo min mutane; tana gargadinsu da su yi tafiya da kyakkyawar imani.”

Ahmed Sulaiman

<[email protected]>