Mata da sana’a

Sana’a ita ce duk wani abu da mutum zai yi domin ya samu na goro, da nufin inganta rayuwarsa.Akwai sana’o’i daban-daban wadanda mata suke yi. Misali dinkin kaya da dinkin kayan adon kawata cikin gida da saka da kitso ko gyaran gashi da sabulu da mai da turaren wuta da kayan kamshi kala-kala.Musamman a wannan […]

Mata da sana’a
Mata da sana’a

Sana’a ita ce duk wani abu da mutum zai yi domin ya samu na goro, da nufin inganta rayuwarsa.Akwai sana’o’i daban-daban wadanda mata suke yi. Misali dinkin kaya da dinkin kayan adon kawata cikin gida da saka da kitso ko gyaran gashi da sabulu da mai da turaren wuta da kayan kamshi kala-kala.Musamman a wannan zamani da muke da cibiyoyin koya sana’o’i daban-daban.

Yana da kyau tun kafin mace ta yi aure, ta koyi sana’a.Wato yadda iyaye suke dagewa yarinya ta yi karatu na addini da na boko haka ya kamata a koya mata sana’a.Amma wannan ba ya nufin a rika dora wa yarinya talla da sunan koyon sana’a.Kamata ya yi a sami wata cibiya da ake koyar da sana’o’in mata a saka yarinya.Idan kuma a gidansu akwai sana’ar da ake yi sai a yi kokari a koya wa yarinya. Domin Kuma wasu mazan ba su yarda da aikin ofis ba.Idan ma suna da sha’wa,ba lallai ne ta samu ba.Domin kuwa akwai matasa maza da mata da yawa da suka gama karatu ,amma aikin ya gagara.Idan aka dubi yadda matasa suke tururuwa duk lokacin da aka kada kararrawar neman ma’aikata ai ya isa ishara.Mutane har mutuwa suke yi a wajen, saboda tsabar yawa,“ Gani ga wane ya isa wane tsoron Allah”.Lallai ya kamata mata su kama sana’a.Domin za ta taimaka musu ta fanni daban-daban na rayuwarsu.koda yake
sukan ci karo da wasu matsaloli yayin da suke kokarin rike sana’o’insu.
Babban abin da yake kawo wa mata matsala game da sana’a shi ne rashin jari.Yana da kyau mace ta fahimci ba sai ta tara makudan kudi ba kafin ta fara sanaa, “ Da rarrafe yaro kan tashi”.Idan ta fara da dan abin da take da shi sai ta ci gaba da tattali tare da fatan Allah ya sanya albarka a ciki.
Wani lokacin kuma akan samu akasi a gurin maza. Domin da zarar wani mijin ya fahimci matarsa tana sana ’a tana dan samun wani abu,to sai ya kawar da kai daga hidimomin gida.Sai nan da nan jari ya karye.A kwai wani mutum matarsa tana aikin gwamnati saboda haka sai ya ce lallai ita ce za ta rika yin cefane tana ciyar da gida.Idan ta yi magana sai ya ce“ Ai ba daga gidan ubanki kika zo da kudin ba”.Y a manta cewa shi Allah ya dora wa hakkin ci da sha.Wasu mazajen kuwa sukan kwace kudin matansu da sunan rance ko bashi.Da haka har sai sun ga jarin matansu ya karye.
Wani lokaci kuma matan da kansu suke karya jarinsu.Idan ba ki da gashin wance kada ki ce za ki yi irin kitson wance.Mata da yawa sukan matsanta wa kawunansu cewa duk abin da suka ga kishiyarsu ko kawarsu ko makwabciyarsu ta yi,to wajibi sai sun yi.Saboda haka sai su kwashe dan jarin nasu su yi abin da bai zama dole ba.Wasu matan kuwa duk abin da suka mallaka yana karewa ne a wajen bokaye da malaman tsubbu.Wasu lokutan kuma girman kai yakan hana mata yin sana’oi .Yayin da wasu sukan ce ai ba su Allah ya dora wa nauyin ciyar da gida ba.Tabbas haka ne.Amma idan aka yi tunani,za a fahimci rayuwa ba ta da tabbas,idan mu ne yau, ai gobe ba mu ne ba.Mace za ta iya mutuwa ta bar miji da ’ya’ya,haka nan shi ma zai iya mutuwa ya bar ta ’ya’ya.
Ya kama maza su daina sa ido a kan abin da matansu suka mallaka.Domin kuwa su ne shugabanni da Allah ya dora hakki iyalansu a kansu.Kamata ya yi su rika taimaka wa matansu domin inganta sana’o’insu kamar yadda wasu mazan suke yi.
Su kuma mata su rike sana’o’insu da muhimmanci ,kada su rika cinye jarin da gan-gan.kuma kada su rika raina jarinsu.Su daina kai wa bokaye kudinsu ba gaira babu dalili.Ya kamata mata su sani Allah shi ne mai juya al’amura a duk lokacin da ya so, amma ba boka ba.Wannan zai taimaka musu wajen gudanar da rayuwar aurensu ba tare da fuskantar matsaloli masu yawa ba.
Kada mata su yi watsi da neman ilimin addini da na boko, domin shi ne gishirin zaman duniya.Kuma da wannan ilimi za su yi amfani su sarrafa sana’o’insu cikin nasara.