Mata da shafukan sada zumunta
Shafukan sada zumunta suna daga cikin abubuwan da jama’a maza da mata ke gudanar da harkokinsu na yau da kullum lura da yadda shafukan ke da sauki da kuma samun biyan bukata cikin sauki yayin amfani da su. Amma mata da dama na fuskantar cin zarafi a shafukan sada zumunta, da ya hada da zagi […]
Shafukan sada zumunta suna daga cikin abubuwan da jama’a maza da mata ke gudanar da harkokinsu na yau da kullum lura da yadda shafukan ke da sauki da kuma samun biyan bukata cikin sauki yayin amfani da su.
Amma mata da dama na fuskantar cin zarafi a shafukan sada zumunta, da ya hada da zagi da cin mutunci wasu lokutan ma har da barazana. Hakan ya sa mata da yawa daina mu’amala da shafukan ba don ba su da abin yi ko wallafawa ba sai dai don cin zarafin da suke cin karo da shi yayin gudanar da harkokinsu a shafukan.
Akwai dalilai da dama da suke sa mace ta yi mu’amala da shafukan sada zumunta da suka hada da:
- Sanin halin da duniya ke ciki, ta hanyar duba labaran jaridun da suke shafukan.
- Isar da wani sako mai muhimminci zuwa ga al’umma, hanyar Intanet ita ce hanya mafi sauki wajen isar da sako ga dimbin jama’a cikin kankanen lokaci.
- Kasuwanci, mata da dama na amfani da shafukan domin tallata hajarsu, lura da yadda komai ke tafiya da zamani a yanzu, shafukan sada zumunta manya hanyoyi ne kuma mafiya sauki wajen tallata sana’a da mata da dama ke amfani da wannan damar wajen bunkasa kasuwancinsu har zuwa wuraren da suke nesa da su wasu lokutan ma har zuwa kasashen waje.
- Sada zumunta, akwai mutane da kun dade da rabuwa da su, ta hanyar shafukan sada zumunta akan iya haduwa a ci gaba da zumunta.
Wadannan kadan ke nan daga cikin dalilan da ke sa mata yin mu’amala da shafukan sada zumunta. Sai dai a ko’ina ana iya samun wanda yake abu da manufa marar kyau, ma’ana akwai wadansu matan da ke amfani da shafukan da wata manufa ta daban. Amma kashi mai yawa na mata wadannan dalilan ke sa su yi amfani da shafukan.
Abin takaici, mata da dama sun daina amfani da shafukan duk da cewa suna da dalilai masu kyau na yin amfani da su. Duk macen da ka ga tana mu’amala da shafukan to ba karamar gwarzuwa ba ce, domin takan hadiye duk wani cin mutunci da zagi domin ta yi abin da ta sa a gaba, amma da yawa sukan sare su kuma daina.
Me ya sa mata ke fuskantar irin wannan kalubale? Kuma ba iya ’yan mata ba hatta matan aure masu mu’amala da shafukan na fuskantar irin wannan kalubale, na yawan damunsu da sakonni, kiran waya ko kiran bidiyo (bideo call), wadansu a yi amfani da hotunansu a bude shafi, ko a wallafa wani labari marar dadi ko na batsa kuma a dauki hoton wadda ba ta ji ba ba ta gani ba a sanya.
To, su ma matan ya kamata su rika taka-tsantsan wajen sanin irin hotunan da za su wallafa a shafukan.
Wace riba kake tunanin za ka samu in ka ci zarafin mace? Ya kai dan uwa! Idan har ka san kana irin haka to ka dubi girman Allah ka daina, kana da kanwa ko ’ya ko mata idan daya daga cikinsu aka yi wa haka na tabbata ba za ka ji dadi ba.
Ke ma ’yar uwa ban bar ki ba; Don Allah ki kyautata mu’amalarki a shafukan nan kuma ki ci gaba da abin da kike muddin bai ci karo da shari’a ba.
Hauwa Shu’aibu Gaya, Kano [email protected](09050782358)