Mata da shaye-shaye: Iyaye da hukuma a tashi tsaye
Mun riski kawunanmu a wani zamani mai cike da abubuwan ban mamaki da takaici ta fuskoki da dama, abubuwa marasa dadin ji sai kara bayyana suke cikin wannan al’umma, daga wannan sai wancan abin dai ga shi nan barkatai, wani abin da yake daukar hankalina shi ne yadda a wannan lokaci mata ma ba a […]
Mun riski kawunanmu a wani zamani mai cike da abubuwan ban mamaki da takaici ta fuskoki da dama, abubuwa marasa dadin ji sai kara bayyana suke cikin wannan al’umma, daga wannan sai wancan abin dai ga shi nan barkatai, wani abin da yake daukar hankalina shi ne yadda a wannan lokaci mata ma ba a bar su a baya ba wajen sanya kawunansu cikin mummunar dabi’ar shaye-shayen kayan maye, hakika wannan ba karamar barazana ba ce ga tarbiyyar matan da suke rayuwa a wannan lokaci da kuma wadanda za su zo nan gaba, idan ba a an yi wa tufkar warwara ba lokaci zai zo da za a kasa fahimtar inda al’umma suka dosa, ma’ana komai zai kasance gaba da baya ko kuma kasa a sama.
Lokutan baya ba mu san haka a cikin al’ummarmu ba, amma a wannan lokaci abin sai kara kamari yake yi, kamar wata wutar daji ko gobara daga kogi, babban abin da yake kara tayar mini da hankali shi ne masu irin wannan hali ‘yan makaranta ne wadanda su ne ya cancanta su san illar hakan da irin cututtukan da hakan ke haddasawa, amma su ne gaba-gaba wajen lalata tarbiyyarsu, walau saboda rudin duniya da rashin tunanin abin da hakan zai haifar musu a rayuwarsu, ko kuma rashin sanin ciwon kai.
Na karanta wani labari a wannan jarida ta Aminiya cikin ‘yan kwanakin baya game da kama wasu ‘yan mata da rundunar hisba ta yi a wani gidan cin abinci, inda suke yawon ta zubar, abin da ya kara daga mini hankali shi ne, yadda bayan dan jarida ya tambaye su shin ko suna shaye-shaye? Wata a ciki ta ce ita tana shan syrup ne kawai, dayar kuma ta ce tsakaninta da Allah giya kadai take sha. Ita tana ganin ai shan kamru uwar laifi ba wani abin a zo a gani ba ne, tun da har tana ikirarin sai ta shafe tsawon wata guda ba ta sha ba, ka ji wani rashin tunani da rashin sanin ciwon kai. Abin takaici da kuma daga hankalin shi ne, tun muna jin labarin a wadansu kasashe da kuma garuruwan da ke nesa da mu yanzu abin ya zo har garuruwanmu, kai ya ma shigo unguwanninmu. Al’amarin ya ma cika gidajenmu.
Na yi imani da Allah mafi yawan masu wannan dabi’a suna daukar kawunansu a matsayin wadanda suka waye, suka san dawar gari, suke ganin kuma kwanjinsu da wuyansu sun yi karfi a sahun nuna wayewar, hakan ne ma ya sa duk macen da ba ta da irin wannan halayya ta shaye-shayen kayan maye idan ta shiga cikinsu za ta zama bagidajiya, idan kuma ta kasa kai zuciyarta nesa sai ta tsunduma ta zama ana damawa da ita.
Wallahi yanzu idan ina fama da mura har kunya nake ji na je shagon magani na ce a ba ni maganin mura na ruwa, sai idan likata ne ya rubuta mini, domin wadannan magunguna su ne suke amfani da su a matsayin kayan maye, likita yana ba da umarnin a sha cikin cokali sau biyu ga marar lafiya, amma su kuma sai su kafa kai su kwankwade wannan kwalbar, daga nan kuma sai kai ya fara daukar caji.
Za mu ci gaba.