Mata da shaye-shaye: Labarin Halimar Jos (10)

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili mai albarka. Muna fata kuna cikin koshin lafiya. Wannan makon shi ne ya kawo mu makon da zan kammala wa masu karatu labarin Halimar Jos. Muna fata kuna daukar darussan da suke kumshe cikin labarin. Ina kara jaddada wa masu karatu cewa wannan labarin ya faru […]

Mata da shaye-shaye: Labarin Halimar Jos (10)
Mata da shaye-shaye: Labarin Halimar Jos (10)

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili mai albarka. Muna fata kuna cikin koshin lafiya. Wannan makon shi ne ya kawo mu makon da zan kammala wa masu karatu labarin Halimar Jos. Muna fata kuna daukar darussan da suke kumshe cikin labarin. Ina kara jaddada wa masu karatu cewa wannan labarin ya faru da gaske. A sha karatu lafiya.

Shigowar da abokin aikina Ibrahim Hassan ya yi ne ya sanya Halima ta dakata dangane da labarin da take ba ni, ganin ina tare da bakuwa sai ya daga mini hannu ya fita, bayan ya fita ne sai ta ci gaba da ba ni labarin:
“Har yamma ta yi Yasir ya bukaci mu tafi gida ba na cikin hayyacina. Haka muka kama hanya tun daga Bauchi har zuwa Jos ban san dawar garin ba, sai da ya taba ni sannan na fahimci har mun iso gida, har ma ya yi wa motar matsugunni. A daren ranar kasa barci na yi, na rika tunanin yadda abotarmu ta kasance.
“Ganin na kasa barci ne ya sanya Yasir ya rika yi mini kalaman kwantar da hankali, hade da nuna mini babu abin da zan iya yi mata a halin yanzu idan ba yi mata addu’a ba. Amma duk wata damuwa da zan sa kaina Mufeeda dai ta riga ta mutu, babu kuma wani kokari da zan iya yi wajen dawo da ita, mu ma kanmu jiran lokaci muke yi, haka dai ya rika yi mini kalamai har na yi ajiyar zuciyar hade da jan dogon numfashi. Ni dai ba zan iya cewa ga lokacin da barci ya dauke ni ba, na dai farka na ga Yasir ba ya nan, na kuma san bai tashe ni ba ne don ya san ba karamin dauki ba dadi na yi kafin na iya barci ba. Bayan na duba agogo ne na ga karfe 10 na safe. Na tashi, na shirya ta hanyar yin wanka da kuma dafa abin da zan ci, amma sam na rasa dandanon abinci.” Ta yi shiru tana mayar da numfashi, a lokaci guda tana kallon zoben da ke karamin dan yatsanta na dama. Na kalli zoben a lokaci guda na kawar da kallona daga zoben zuwa ga kallon jaridar Aminiya da ke kusa da ni.
Jin ta yi gyaran murya ne sai na sake tattara kallona zuwa gare ta, inda ganin hakan ya sanya ta ci gaba da ba ni labari: “Ina zaune tarin abinci a gabana na kasa ci, sai na ji wayata ta shiga kadawa, daga farko kamar ba zan amsa kiran ba, wata zuciyar ta ce mini in dauka, daf da wayar za ta tsinke ke nan na dauki wayar ba tare da duba wanda ya bugo ba. Aka yi sallama, na amsa ciki-ciki, a nan ta sanar da ni Maryam ce. Maryam kawata ce tun a jami’ar Maiduguri, inda ta karanta aikin likita, daga baya ta kware a bangaren mata, tun muna jami’a ustaziya ce, don ita ce Amirar jami’ar ma a lokacin. ‘Yar Jihar Kaduna ce, ganin cewa ita kullum wa’azi, sai in rika guje mata, duk da tana damuwa da hakan, amma kasancewar tana matukar ji da ni sai hakan bai sa ta guje ni ba. Ko lokacin aurena ma ta zo, inda ta rika ba ni shawarwari.
“Na yi kokarin sake muryata don kada ta fahimci ina cikin damuwa, muka gaisa, sannan nake sanar da ni ta samu canjin wurin aiki daga Kaduna zuwa Jos, har ma ta tare, inda aiki ya hana ta tuntuba ta sai yanzu, don haka in kasance da shirin karbar bakuwa a ranar Lahadi mai zuwa. Na sanar da ita babu damuwa, muka yi sallama.
A ranar Lahadin da ta zo ne ta fahimci ina cikin halin dimuwa da damuwa, hakan ya sanya ta yi amfani da tausasan kalamai har ban san lokacin da na sanar da ita dukkan matsalata ba, tun daga rashin haihuwa da kuma irin rayuwar da na yi har zuwa mutuwar Mufeeda. A ranar babu irin nasihar da ba ta yi mini ba, ta bukaci in fawwala wa Allah (SWT) komai, in tabbata a zuciyata Shi ne mai iko a kan komai, kuma a dukkan wani tsanani akwai sauki, sannan in fahimci kowane dan Adam akwai yadda ake jarraba shi, mai hakuri da juriya shi ne mai cin riba.  Hakan ya sanya na fara tunanin komai na rayuwa mai faruwa da karewa ne. Babu abin da yake tabbata, duk abin da mutum ya aikata zai samu sakamakonsa, wadansu tun a duniya ma suke gane makomarsu. Idan ka aikata alheri za ka ga alheri, hakan idan ka aikata sharri za ka ga gani a kwaryarka.
“Dawowar Maryam Jos ya zame mini alheri, domin ta ci gaba da yi mini nasiha, hade da kalaman karfafa mini gwiwa, ya kasance na shiryu, ni ce azumin nafila, sallah ba ta wuce ni, na yawaita sadakoki, na kasance mai yawan kyauta, na kuma rika istigfari wajen neman gafara a wurin Ubangiji, sannan ta hada ni da wani maigidanta a wurin aiki, kwararren likitan mata ne, shi ne ya yi mini gwaje-gwaje da ba ni magungunan da zan yi amfani da su, a karshe Allah Ya yi ikonsa na samu ciki, haka na rika zuwa asibiti ana ba ni dukkan shawarwari har a karshe Allah Ya sanya na haifi tagwaye, mace da namiji. Inda a yanzu suke cikin koshin lafiya.”
Bayan ta yi shiru ne, sai ta kalle ni, inda na rika kallonta ina girgiza kai, hade da lissafa darussan da ke cikin labarin. Ganin na ci gaba da kallonta ne, sai ta ci gaba da magana: “Na kasance mai karanta Aminiya fiye da shekara biyar, na kuma kasance ina biye da rubuce-rubucenka, wannan dalilin ya sa na ga dacewar in ba ka labarina don ka yada shi a duniya, don ya zama babban darasi ga ‘yan baya.” Na yi mata godiya, daga nan muka yi sallama ta fita. karshe.
Domin karin bayani za a iya tuntubar Bashir Liman a wannan lambar 07036925654.