Mata da shaye-shaye: Labarin Halimar Jos (2)

Bayan ya fita ne sai na bude dirowata sannan na fito da wani kofin glass, na kalli cikinsa, daga nan na goge cikinsa da tissue paper, sannan na mika mata kofin. Ta karba ta ajiye shi a kusa da Maltinar da ke gabanta. Na rufe dirowar, sannan na mayar da hankalina gare ta. Ta gyara […]

Mata da shaye-shaye: Labarin Halimar Jos (2)
Mata da shaye-shaye: Labarin Halimar Jos (2)

Bayan ya fita ne sai na bude dirowata sannan na fito da wani kofin glass, na kalli cikinsa, daga nan na goge cikinsa da tissue paper, sannan na mika mata kofin. Ta karba ta ajiye shi a kusa da Maltinar da ke gabanta. Na rufe dirowar, sannan na mayar da hankalina gare ta. Ta gyara zama, sannan ta fuskance ni.
“Na shiga jami’a da burin in yi karatu don in taimaki iyayena, kasancewar na san yadda suke fadi tashi wajen ganin sun kyautata mini ciki har da biya mana kudin makaranta, kasancewar a lokuta da dama idan mahaifinmu ya karbi albashinsa, ya biya mana kudin makaranta, yakan zauna ba shi da ko taro, na tuna lokacin da ya yi shekara da kaya kala uku. Na fara canzawa ne a lokacin da na hadu da kawata Mufeeda, a lokacin muna mataki na uku a Jami’a. Mufeeda babbar yarinya ce, mai jan aji da kuma nuna isa, kullum tana cikin shigar kasaita. Wata rana jarrabawa ta hada ni zama kusan wuri daya da ita, tana zaune a bayana, ka san ba ni da buri a lokacin face in yi karatu, don haka ina daga cikin na gaba-gaba wajen samun kyakkyawan sakamako a ajinmu, ganin ina rubutu ba kama hannun yaro, sai na ji ana taba ni da biro a bayana, na kirmishe, na ci gaba da rubutuna. Maimakon a daina taba ni sai na ji wannan karon har da zungura ta da kan biro. Na jiyo a fusace, muka hada ido da ita, sai ta yi mini murmushi.
“Na juya don in ci gaba da rubutu, sai ta ci gaba da taba ni, na juyo fuska a daure, cikin sigar rada ta ce mini, don Allah in taimaka mata. Na ce mata ta ba ni lokacin kadan, da yake a lokacin na kusa kammala amsa dukkan tambayoyin da na zaba don in amsa. Bayan wani lokaci ne sai na daga mata ta rika kwafa, har zuwa lokacin da aka ce lokaci ya yi, na je na mika takardar da na amsa jarrabawata, sannan na fita daga dakin jarrabawar.
Ta ce: “Ina cikin tafiya ke nan, sai na ji ana cewa malama, na kalli mai yi mini magana, sai ya ce mini ana yi mini magana a baya, bayan na juya ne sai na ga ashe Mufeeda ce, na tsaya ina kallon shigar alfarmar da ta yi har ta karaso wurin da nake. Ta kalle ni, wanda hakan ya sanya na kalli kaina, sanye nake da kodaddiyar atamfa, da wani takalmina da ya aka yi gasar dinki a kansa. Na kawar da kallona daga kan takalmin cikin takaici, a lokaci guda na kalle ta. Bayan ta yi mini murmushi ne, sai ta fara yi mini godiya kan taimakon da na yi mata. Na ce mata babu damuwa, duk wanda ya taimaki wani, Allah zai taimake shi.” Ta yi shiru, sannan ta fara daidaita numfashinta.  
Ki sha Maltinar mana kafin sanyinta ya gudu.” Na ce da ita cikin murmushi. Bayan ta yi murmushi sai ta ce, “sanyin ma na gudu ne?” Cikin dariya na ce mata, “Ki yi wasa ki gani idan bai gudu ba.” Hakan ya sanya ta bude Maltinar sannan ta tsiyaya ruwan Maltinar zuwa rabin kofin gilashin. Na kalli agogon bangon da ke ofis din a lokacin da take shan Maltinar. Bayan ta shanye ne, sannan ta ajiye kofin sai ta ci gaba da magana:
“Daga nan ne na ga tana bude jakarta, sannan ta ciro kudi ta mika mini. Na tsaya ina kallonta ba tare da na karba ba, ta ce mini ba wai na ba ki don in biya taimakon da kika yi mini ba ne, a’a, na yi miki ne saboda da Allah. Ta tsaya tana kallo na, ganin ban karbi kudin ba sai ta ce mini, in tambaye ki mana? Bayan na kalle ta, ke ce kika tambaye ni kudi? Na girgiza kai. Ta ce mini to kyauta na ba ki. Ta bude jakata ta tura kudin a ciki, duk da cewa a cikin zuciyata har na fara kasafin abubuwan da zan saya da kudin, amma a fili sai na nuna jan ajina. Bayan ta sanya kudin ne, muka yi sallama.”
Ta yi shiru, bayan kira ya shigo wayata, na kalli wayar sannan na dauka, nan aka kashe, bayan na kalle ta sai na ce mata ‘flashing’ aka yi.
Daga nan ta ci gaba da magana:
 “Bayan mun yi sallama ne, sai na fara tafiya, daga nan na nufi shagon cin abinci, a cikin shagon cin abincin na kirga kudin da ta ba ni, dubu 10 ne, farin ciki ya mamaye birnin zuciyata. Na yi odar abinci mai rai da lafiya. Na take cikina.” Ta gyara zama, inda hakan ya sanya ni ma na muskuta, na bude dirowata na dauko mintin Splash na bare ledarsa, sannan na jefa bakina.
Ta ci gaba da magana: “Daga nan ba mu kara haduwa da ita ba,”, bayan ta tsahirta: “Wata rana na fito daga dakin karatu sai na ji wata mota tana yi mini hon, daga farko ban damu in saurara ba, domin a iya sanina babu wanda na sani da zai yi mini hon a cikin mota irin wannan mota ta alfarma. Ganin bai saurara ba ne. ya sanya aka je gaba da ni kadan, sannan aka yi wa motar matsagunni. Ta fito daga cikin motar. Mufeeda ce sanye da doguwar bakar abaya, ta suturce gashin kanta da hadadden gyale ruwan hoda, ta nufo inda nake tana murmushi hade da tafiyar kasaita, na mayar mata martanin murmushin da ta yi mini. “Kin yi wuyar gani, ganinki sai an cika fom,” ta ce da ni bayan ta karaso wurin da nake. “Ba haka ba ne,” na ce da ita. “Mene ne to?” Ta tambaye ni.