Mata da shaye-shaye: Labarin Halimar Jos (3)

Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya amfanar da mu duk bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga cigaban bayani kan hanyoyin sulhunta ma’aurata. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma Ya amfanar da su, amin.Bayan Ma’aurata […]

Mata da shaye-shaye: Labarin Halimar Jos (3)
Mata da shaye-shaye: Labarin Halimar Jos (3)

Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya amfanar da mu duk bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga cigaban bayani kan hanyoyin sulhunta ma’aurata. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma Ya amfanar da su, amin.
Bayan Ma’aurata ko magabatansu sun zabo amintattun mutane biyu da suka cika dukkan siffofin da muka ambata, kuma suka amince da su yi wannan aiki to sai a sa rana da wurin yin wannan zaman alkalanci.
Matsayinsu:
Matsayin wadannan mutum  biyu da karfin ikonsu kamar matsayin da karfin ikon alkali ne, domin haka Allah Ya kira su a cikin Alkur’ani Mai girma da kalmar HAKAMAN, watau masu alkalanci ko masu shiga tsakanin don daidaita sabani tsakanin mutane, bai kira su da wakilai ba;  don haka duk hukuncin da suka zartas a bayan zaman alkalancin nan to ya tabbata kuma dole ma’aurata suyi aiki da shi ko da bai masu dadi ba.
Aikinsu:
*Kyautata niyya: Alkalan biyu su fahimci cewa akwai gagarumin aiki a gabansu don haka wajibi ne akansu suyi dukkan kakarinsu, su kai su kawo wajen ganin cewa sun shirya ma’auratan nan sun dawo suna zaman lafiya da aminci a tsakaninsu: kamar yadda Allah Madaukakin Sarki Ya fada cewa: …Idan sun yo nufin gyarawa, Allah zai daidata tsakaninsu…
Watau in sun alkalan sunyi nufi kuma sun yi niyyar gyara wannan auren, to Allah zai daidata tsakanin ma’auran ta hannunsu. Don haka in suka kyautata niyyarsu, wani sinadari da zai tabbatar masu da cin nasarar aikin dake gabansu.
*Alkalan biyu za su zauna tare da ma’auran su tattauna da su game da husumar da ke tsakaninsu. Haka kuma za su zauna da su daya bayan daya daban-daban, zasu zurfafa bincike, za su zauna da wasu daga cikin magabatan ma’auran, ko aminansu ko wasu ‘yan”uwa duk don kokarin samun hakikanin bayani kan husumar da kuma samun kwakwkwaran hujjar da za su kafa wajen yanke hukunci game da wannan aure.
*Su dage da zurfafa bincikensu kadda su gajiya; su sami kwarin gwaywa da wannan zance na Ubangiji Madaukakin Sarki; Aya ta 114 cikin suratun Nisaa’i:  “Babu wani alheri a cikin ganawarsu face wanda yayi umarni da wata sadaka ko kuwa wani alheri ko kuwa gyara tsakanin mutane. Wanda ya aikata haka domin neman yardodin Allah, to zaMu ba shi lada mai girma.”
Don haka aiki da Allah Subhanahu wa Ta’ala Ya sanya masa tambarin alkhairi da samun lada mai yawa wacce kila ma ta yi sanadiyyar shigarsu Aljannah.
*Kar su bi son ra’ayin daya daga cikin maauratan sai dai su bi gaskiya koda daya daga cikin ma’auratan bai so ba.
In sun aminta akan hukunci daya to za a zartar da shi a matsayin doka a kotun musulunci ko gaban wani shugaba, in kuma suka bada hukunci daban-daban to ba za a zartar da shi ba.
*In sun tabbatar rabuwar aure shine kadai hanyar kwantar da husumar nan, to suna da damar su raba wannan auren a ra’ayin mafi yawan Malamai. Allah Ya fada cikin Ayah ta 128 Suratun Nisaa’i cewa yin sulhu da daidaitawa tsakanin ma’aurata shin mafi alheri sama da mutuwar aure, amma kuma in sulhun ya gagara, rabuwar aure ta zama dole, to itama rabuwar auren Allah Yasa mata alheri inda yace, a cikin Aya ta 130; Suratun Nisaa’i:
“Kuma idan sun rabu, Allah zai wadatar da kowannensu daga yalwarsa…”
*In binciken wadannan alkalai biyu ya nuna masu laifin daga wajen uwargida ne, itace taki sauke wasu nauye-nauyen auratayya dake kanta, to sai alkalan nan guda biyu suyi umarnin khul’i, watau ta biya kudi, shi kuma ya sakke ta.
In kuma suka fahimci matsalar daga wajen Maigidan ne, saboda yaki sauke wasu hakkokin auren da suka rataya akanshi ko makamancin haka, to sai suyi umarnin ya sakketa ba tare da ta biya shi kudi ba.
In kuma matsalolin daga duka bangaren biyune, to alkalan nan biyu suna da ikon raba don kwantar da wannan husuma.
*Hukuncin da suka yanke sai su mika shi ga alkali ko shugaba shi kuma ya zartar da shi a dokance.
Sai sati na gaba in sha Allah. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarsa a kodayaushe, amin.