Mata da shaye-shaye: Labarin Halimar Jos (6)
Halima ta juyo ta kalle ni, na yi mata murmushi, don in nuna mata ina biye da ita, hakan ne ya sanya ta ci gaba da magana:“Ganin na yi masa wani irin kallo ne sai ya jawo ni jikinsa, na kwanta a jikinsa kamar yadda mage take kwantawa a jikin mai ita. Ya kalle ni, […]
Halima ta juyo ta kalle ni, na yi mata murmushi, don in nuna mata ina biye da ita, hakan ne ya sanya ta ci gaba da magana:
“Ganin na yi masa wani irin kallo ne sai ya jawo ni jikinsa, na kwanta a jikinsa kamar yadda mage take kwantawa a jikin mai ita. Ya kalle ni, na ga ya yi wani irin murmushi, na yi masa murmushi, bayan na kalli Mufeeda ne sai ta kashe mini ido. Haka na ji ya fara shasshafa ni. Ni dai ban san dawar garin ba, na dai farka na gan ni kwance a kan gado babu kaya a jikina. Na tashi da sauri, na shiga ban daki, bayan na yi wanka ne na sanya kayana sai na shiga tunanin yanzu fa an fasa kofar budurcina, da yake shaidan ba shi da dama, sai ya ci gaba da zuga ni ai kuwa ni ma na ji dadi, bugu da kari, yanzu zan zama mai kudi kamar Mufeeda, ina cikin tunani ne sai ga Alhaji ya shigo rike da kofin shayi.”
“Barka da asuba.” Ya ce da ni yana murmushi. Sai a lokacin na fahimci ashe gari ya waye. “Ina kwana.” Na ce masa. Ya amsa yana murmushi. Bayan ya yi mini wani irin kallo, “Ashe ke ma ta gasken ce, samun irinki sai an dage…” Na ci gaba da kallonsa. “Kin mayar da ni sabo jiya, kin sanya zuciyata kara afka wa cikin kogin sha’awarki.” Na yi dariya, bayan ya kurbi ruwan shayin ne, ya ci gaba da magana. “Zan iya cewa na fi kowa sa’a a duniya, dalili kuwa shi ne, sakamakon haduwata da ke.” Na kalle shi na yi dariya, “Sai nan gaba ne za ki gane hakan.” Ya ce da ni bayan ya nufo inda nake. Na dai ci gaba da kallonsa.
“Ina Mufeeda?” Na tambaye shi bayan ya iso wurin da nake. kwankwasa kofar da muka ji ana yi ne ya sanya bai ba ni amsa ba. “Shigo.” ya ce kai tsaye ba tare da ya tambayi wanda ke kwankwasa kofar ba. Mufeeda ta tura kofa ta shigo. Na ji dadin ganinta, bayan mun gaisa ne, Alhajin ya ci gaba da koda ni, inda Mufeeda ma ta rika zuga ni. Daga nan ya ce mini in shirya mu je ya yi mini sayayya. Haka aka yi duk abin da nake so sai da ya saya mini. Sannan ya kawo kudi mai yawa ya ba ni. Ta dalilin Alhaji na je Dubai da Landan da Faransa da Amurka da sauran kasashen duniya.
Daga nan ne fa na shiga harkar gadan-gadan bayan na fahimci kudin da ake samu, amma Mufeeda ta kasance mai zuga ni kamar yadda makamashi ke rura wuta. Bayan wata daya ne ban ga al’adata ba, hankalina ya tashi, domin na san kwanan zance, wato na dauki ciki, kuma hakan ya faru ne tun abin da ya faru a daren farkon haduwata da Alhaji. Na sanar da Mufeeda, maimakon in ga hankalinta ya tashi sai na ga ta yi dariya. “Mugunta ko?” Na tambaye ta raina a bace. A lokacin da take dariya, “Ke don wannan ne sai hankalinki ya tashi? Mene ne a ciki? Ki sha kuruminki za mu yi wa tufkar hanci.” Na dai ci gaba da saurarenta. Ba tare da bata lokaci ba sai na ga ta bude jakarta, ta ciro wadansu kwayoyi ta ba ni. Na karba sannan na ci gaba da kallonta. “Kin dai ci abinci ko?” Ta tambaye ni bayan na karbi maganin. Na gyada mata kai, daga nan ta ciro robar ruwa daga jakarta ta ba ni. “Ki sha biyu daga ciki, sauran sai ki ajiye.” Ta fada mini a lokacin da take kallon kwayoyin maganin da ke hannuna. Na jefa kwaya biyu a bakina, sannan na bi su da ruwa. Bayan na shanye maganin. “In dai wannan matsalar ce, an shawo kanta.” Ta ce da ni. Na yi dariya.
Daga baya ne take sanar da ni akwai budurin da Alhajinta zai shirya mata jibi, don haka dole a yi shigar kece raina, ta kawo wannan bayani ne don ta kwantar mini da hankali, don kuma in kara sake jiki. A ranar da na sha maganin babu irin ciwon da marata ba ta yi ba, daga nan na rika wani irin fitsari marar kyawun gani. Na sha wahala, amma dai cikin ya zube. Wani abu da Alhazan da muke mu’amala da su suke so shi ne, dukkansu ba sa son yin amfani da kwaroron roba, amma duk kudin da kake so za su ba ka.
Haka Alhaji ya rika yi mini ciki ina zubarwa ta hanyar shan magani, a gaskiya na tara abin duni=ya ta wannan hanyar, domin na mallaki gida a Maiduguri da Kano da Kaduna, sannan na gina gida mai kyau a Jos, inda muka tare da mahaifiyata, daga baya ta daina tuyar masa. Ko bayan na kammala jami’a har na yi hidimar kasata a Kaduna ma ban daina harkar ba. A irin harkar ne na hadu da wani saurayi da yake matukar sona, ya kuma bijiro mini da maganar aure saboda yadda na kware wajen iya kwanciya, na amince masa, kasancewar na san ba zan sha wahala ba, domin gidansu akwai masu gidan rana, sai dai na shiga tasku da tsamomouwa bayan aurenmu da shi.
Za mu ci gaba.