Mata da shaye-shaye: Labarin Halimar Jos (7)

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili mai albarka. Ga ci gaban labarin da muke kawo muku makonni 6 da suka gabata. Muna fata kuna daukar darussan da suke kumshe cikin labarin.A kokarin gyara zaman da nake yi ne ya sanya Halima ta yi shiru, muka hada idanu, na yi mata murmushi, bayan […]

Mata da shaye-shaye: Labarin Halimar Jos (7)
Mata da shaye-shaye: Labarin Halimar Jos (7)

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili mai albarka. Ga ci gaban labarin da muke kawo muku makonni 6 da suka gabata. Muna fata kuna daukar darussan da suke kumshe cikin labarin.
A kokarin gyara zaman da nake yi ne ya sanya Halima ta yi shiru, muka hada idanu, na yi mata murmushi, bayan ta mayar da martani ne, na ce mata: “Ina saurarenki.” Ta sake yin murmushi, ta gyara zama, sannan ta ci gaba: “Bayan an daura aurena da Yasir ne muka tare a gidansa da ke G.R.A, mun ci soyayya domin ban taba jin son da namiji a duniya kamar na Yasir ba, babu abin da yake bukata ban yi masa ba, na zama masa sanyi a lokacin da ya dauki zafi, na zama masa inuwa a lokacin da yake rana, na kuma kasance mai sanyaya masa a lokacin da ya dauki zafi. Na yi amfani da abin da yake so wajen cafke shi, na kasance mai taba masa duk inda yake so a matsayin wani sirrina na burge shi, na ba shi duk abin da yake so a wurina don in mallake shi. Na yi duk abin da nake so da kudinsa, domin mahaifinsa akwai gidan rana.” Halima ta fara tari, na yi mata sannu, ta zuba ruwa a kofin gilashin da ke gabanta, na rika danna wayata a lokacin da take shan ruwa, daga nan na duba lokaci, ganin ta ajiye kofin gilashin ne sai na kara tattara hankalina gare ta.
Bayan ta kalli robar ruwan da ke gabanta ne sai ta ci gaba da magana: “Na fara shiga matsala ne bayan mun shekara 5 ba mu samu haihuwa ba, kwatsam wata rana mahaifiyar Yasir ta shigo gidanmu kamar an wullota, a lokacin Yasir baya nan, ta yi mini kaca-kaca. Ta ce: “Ba mu san ke juya ba ce da ba za mu bari danmu ya aure ki ba, babu abin da kika iya sai dai ki ci ki yi kashi, ga mata nan suna haihuwa, amma ke ko batan wata ba ki taba yi ba.” Na yi shiru ina kallonta, a lokaci guda zuciyata na tafarfasa kamar za ta fashe. Haka ta gama yi mini kaca-kaca ta fita daga gidan. Tun da ta fita na kasa motsawa, tunani iri-iri babu wanda bai zo mini ba. Daga baya ne na kira Mufeeda don in sanar da ita sabuwar duniyar tasku da na fada, amma lambarta ba ta tafiya, kasancewar ita har a wannan lokacin ma ba ta yi aure ba, a lokacin babu abin da take yi sai kawalci, inda take kai wa Alhazai da samari mata su kuma su biya ta. Haka dai na wuni a ranar ina neman Mufeeda don in sanar da ita halin da nake ciki, amma wayarta ba ta tafiya.”
Ta sake yin shiru, wanda hakan ne ya sanya na ce mata: “Ina biye da ke.” Ta kara yin murmushi, sannan ta ci gaba:
“Bayan Yasir ya dawo ya fahimci yanayina ya canza, babu irin tambayata da bai yi don in sanar da shi dalilin fadawata tafkin damuwa ba, amma na ki in sanar da shi, na dai ce masa ba na jin dadin jikina, amma cikin zuciyata na san ko ba dade ko ba jima mahaifiyarsa za ta tunkare shi da maganar. Haka dai na rika shan tsangwama iri-iri daga wurin dangin mijina.”
Ta sake yin shiru, sannan ta hada rai, wanda hakan ya nuna mini abin da za ta sanar da ni lallai ya karci zuciyarta har ya yi mata rauni. Ai kuwa hasashena ya zama gaskiya. daga nan ne ta ci gaba da magana: “Da yake dangin mijina sun samu daurin gindin a wurin mahaifiyarsa, wata rana yayar Yasir da kannensa suka yi mini dukan tsiya. Suka bar ni magashiyan kwance a kasa babu ko tausayi. Haka aka tafi da ni asibiti, na sha jinya duk a kan rashin haihuwa, inda daga baya likita ya sanar da ni mahaifiyata ta samu matsala, matsalar da sai dai tsananin rabo ta sa in samu karuwa. Yasir ya san kwanan zancen domin shi kansa ya taba yi mini ciki, na zubar, daga bisani na bi sharuddan shari’a idan wani ya yi wa mace ciki har ta kai ga yin aurensu.”
Wayarta ta fara kara, wanda ya sanya hankalinta ya koma cikin jakarta, har ta ciro wayarta a cikin jaka ban daina saka labarin da take ba ni a kwakwalwata ba, bayan ta amsa wayar ta gama ne ta ci gaba da magana:
“Mahaifiyar Yasir ta tilasta masa ya kara aure, dama gidansa babba ne, inda aka hada ni da kishiyata wuri daya, a nan ma na ga tasku iri-iri musamman ma bayan kishiyata ta dauki ciki. Abin duniya ya dame ni. Na kira Mufeeda cikin sa’a na same ta a waya. Ta ce mini tana zuwa washegari bayan na sanar da ita halin da nake ciki. Washegari kuwa sai ga Mufeeda a gidanmu. Ta ba ni shawarar za mu je ta sama mini magungunan da zan rika sha wadanda za su dauke mini hankali har in rika mantawa da damuwata. Na yi farin cikin hakan, domin a lokacin babu abin da ke damuna kamar matsalar rashin haihuwa da  ta cacukwai  kwalar rayuwata.”
Za mu ci gaba.