Mata da shaye-shaye: Labarin Halimar Jos (9)
Ganin ina dariya ne, sai Halima ta yi shiru, sannan ta kalle ni, ganin tana kallona sai na ce mata: “Kin san tunanin me nake yi?” Ta girgiza kanta. Bayan na kalli jakarta, sai ita ma ta kalla, sannan na ci gaba da magana, “So nake in duba jakarki don in dauki maganin da zai […]
Ganin ina dariya ne, sai Halima ta yi shiru, sannan ta kalle ni, ganin tana kallona sai na ce mata: “Kin san tunanin me nake yi?” Ta girgiza kanta. Bayan na kalli jakarta, sai ita ma ta kalla, sannan na ci gaba da magana, “So nake in duba jakarki don in dauki maganin da zai sa ni barci, domin damuwar rashin kudi ta yi mini yawa.” Na fadi hakan ne ta sigar wasa, inda hakan ya sanya ta fara dariya. Hakan ne ya sanya ta ci gaba da ba ni labarin a kan gabar dalilin shiriyarta. Bayan ta natsu a dariyar da take yi ne sai ta ci gaba:
“Na fara shiga hanyar tafiya shiriyata ce bayan wani mummunan al’amarin da ya faru, faruwar al’amarin ya sanya na dawo hayyacina. A ranar da al’amarin zai faru ina zaune sai Mufeeda ta yi mini waya cewa akwai Alhajin da za ta kawo masa wadansu ‘yan mata Jos, don haka in shirya karbar babbar bakuwa, na yi dariyar jin dadi, domin zan samu wata dama ta tattauna yadda zan shawo kan matsalata. Bayan mun kammala wayar sai na tashi don shirya mata girki na musamman, shi kansa Yasir bayan ya tashi daga barci ya lura yanayina ya canza, domin ya gan ni cikin farin ciki. Cikin zamudi ya tambaye ni abin da yake faruwa, na shaida masa cewa, yau dai na tashi cikin farin ciki ne, yanayinsa ya canza, shi ma ya shiga cikin farin ciki, ba ya son damuwata daidai da miskala zarratan. Na yi sa’ar miji, Yasir na sona, dalilin da ya sa ma bai rabu da ni ba ke nan. Ni ma ina matukar sonsa shi ya sa zugar Mufeeda ta in kashe aurena ba ta yi tasiri ba. Bayan ya fita ne na shiga kicin sannan na shirya wa Mufeeda tuwon shinkafa da miyar taushe, kasancewar shi ne abincin da ta fi so a rayuwarta. Daga nan na zauna zaman jiran zuwanta kasancewar na san daga Kano zuwa Jos bai wuce awa uku da rabi ba.
“Na fara shiga damuwa ne ganin yamma ta yi amma ban ji duriyar Mufeeda ba, na kira wayarta amma a kashe. Haka lokaci zuwa lokaci na rika kiran wayarta amma a kashe, hankalina ya tashi domin jikina ya ba ni cewa ba lafiya, musamman ma duk lokacin da na tuna ta sai na ji zuciyata ta buga. Babu munanan abubuwan da zuciyata ba ta saka mini ba. Kwana biyu bayan mun yi Mufeeda za ta zo Jos ba ta zo ba, sai na ji wayata ta fara kadawa, na ga bakuwar lamba, bayan na dauka ne sai na ji muryar mace cikin kuka, daga nan ta ce mini Jamila kanwar Mufeeda ce, jin yadda take kuka sai hankalina ya yi mummunan tashi domin na san ba kalau ba. Cikin kuka ta ba ni labarin hadarin da su Mufeeda suka yi, inda ita da wadansu mata hudu suka kone kurmus, bayan sun yi taho mu gama da wata babbar motar dakon mai a kan hanyar Saminaka zuwa Jos. Na yi mutuwar tsaye, na rasa inda zan sa kaina, gani nake kamar ba gaskiya ba ne, Mufeeda na da ranta, domin ko bayan mun kammala waya da kanwarta ma sai da na kara gwada lambarta a zuciyata ina alla-alla wayarta ta shiga, don ta sanar da ni labarin da aka fada mini ba gaskiya ba ne.
“Bayan Yasir ya dawo gida ne ya gan ni a birkice, na yi yaga-yaga, a kidime ya tambaye ni dalilin fadawata cikin wannan kidimammen yanayi, a cikin kuka na sanar da shi halin da ake ciki, yana tsaye ne lokacin da na ba shi labarin, amma cikin kankanen lokaci ya hada gumi, sannan ya samu wuri ya zauna. Washegari muka shirya don zuwa Bauchi, har a lokacin da muke kan hanya ban yarda ta mutu ba, gani nake wani mafarki nake, wanda nan da kowane lokaci zan iya farkawa. Har muka je Bauchi ban yarda ta mutu ba. Sai bayan mun karasa kofar gidansu na ga taron mutane ana zaman makoki ne ya sanya na fara gaskata batun mutuwar. Ganin mahaifiyarta fuska a kumbure, idanunta sun yi jajawur ne ya sanya na gaskata batun mutuwar, hakan ya sanya wani hawaye mai zafi ya kwararo daga idanuna ya gangaro kumatuna, na gaishe da mahaifiyar marigayiya Mufeeda, a lokaci guda wani bakin cikin na sukwana ta, sannan na zauna kikam na kasa cewa komai, sai tunanin yadda rayuwarmu ta kasance, tun daga jami’a har zuwa mutuwarta, ganin tashin hankalin da nake ciki ne, sai ya sanya aka koma ba ni hakuri.
Don jin shin ko mutuwa za ta kasance wa’azi a wurin Halima sai ku kasance da mu a mako na gaba. Allah Ya kaimu da rai da kuma lafiya, sai makon gobe.