Mata da yara miliyan 40 ne ke bautar zamani – Rahoto

A daukacin fadin duniya akwai mafi yawancin bayin zamani wadanda mata ne da ‘’yan mata, a cewar wani sabon rahoto. Binciken wanda kungiyar kwadago ta Duniya (ILO) ta fitar tare da hadin gwiwar kungiyar takun ’yanci ta Walk Free Foundation, tare da hadin gwiwar kungiyar kaurar Jama’a ta duniya (IMO) suka gudanar, ya yi nuni […]

Mata da yara miliyan 40 ne ke bautar zamani – Rahoto

A daukacin fadin duniya akwai mafi yawancin bayin zamani wadanda mata ne da ‘’yan mata, a cewar wani sabon rahoto.

Binciken wanda kungiyar kwadago ta Duniya (ILO) ta fitar tare da hadin gwiwar kungiyar takun ’yanci ta Walk Free Foundation, tare da hadin gwiwar kungiyar kaurar Jama’a ta duniya (IMO) suka gudanar, ya yi nuni da cewa kimanin mutum miliyan 25 an tursasa musu yin aikin bauta ne, inda wasu miliyan 15 aka yi musu aure dole, bisa kiddigar shekarar 2016.

Mata da ’yan mata su ne kimanin mutum miliyan 29 ko kasha 71 cikin 100 na wadanda bautar zamani ta dabaibaye su a fadin duniya, kamar yaddda yake kunshe a rahoton.

Sabon kiyasibn da aka fitar a lokacin taron Majalisar dinkin Duniya da aka gudanar ranar Talatar da ta wuce a birnin New York na Amurka, ya kuma gano cewa akwai kimanin kananan yara miliyan 152, wadand ashekarunsu suka kama daga biyar zuwa 17 da aka tursasa su yin aikin bauta, kamar yadda alkaluman binciken suka nuna a daidai lokacin.

Rahoton ya yi karin haske kan cewa mutum guda a cikin mutum hudu kananan yara ne da ke dabaibaye da bautar zamani bisa alkaluman shekarar 2016.

Mata ne suka kwashi kasha 99 cikin 100 na wadanda bautar zamani ta tursasa su suka shiga karuwanci, tare da wasu kasha 84 cikin 100 da aka yi musu auren dole, a cewar binciken.