Mata Iyayen Giji?
Ku sani ya ku masu saurare, mace daban take da namiji, mace ta kowace fuska ni’ima ce. Mace tana da taushin murya, tana kuma da taushin jiki kamar reshen itace mai rausayawa. Jikinta in ta yi kwalliya yana kamshi kamar itacen kafur. Hakoranta abin sha’awa ne, a koyaushe suna haske kamar kankara in sun sha […]
Ku sani ya ku masu saurare, mace daban take da namiji, mace ta kowace fuska ni’ima ce. Mace tana da taushin murya, tana kuma da taushin jiki kamar reshen itace mai rausayawa. Jikinta in ta yi kwalliya yana kamshi kamar itacen kafur. Hakoranta abin sha’awa ne, a koyaushe suna haske kamar kankara in sun sha asuwaki. Gashinta bakikkirin yake kamar duhun dare. Kundukukinta mani’imci, fuskarta kamar nunannen baure, nononta kamar ‘ya’yan rumman. Tana tafiya tana rangaji kamar reshen bishiya lokacin da iska ke kada shi, jikinta tattausa, cikinta kamar shafin takobi, goshinta kamar tauraro. Idanunta kamar ruwan raba. Idan ta yi magana sai hakoranta su bayyana kamar danyen lu’ulu’u ne ke numfashi cikin bakinta.
Yarinya mace tana jan zukata da siffarta, idan ta yi murmushi sai ka yi tsammanin hasken wata ne ke walkiya daga bakinta. Idan ta zama wadda gayar kyau ke gare ta, tana harbi da ganin ta. Tana da fatar baki ma fi taushi daga kumfa mafi kamshi da yawu mafi zaki, wane zuma farar saka.
Budurwar yarinya tana da kirji mai tudu wanda ke dauke da manyan nonuwa tamkar gogaggen farin karfe. Haka nan tana da manyan cinyoyi da kowa ke sha’awar gani wadanda suke madaidaita sai ka ce ginshikin lu’ulu’u. Ya kai talaka ka sani mutum ko aljani, manyan sarakuna da masu tsananin iko ba sa iya sarauta ko nuna iko ba tare da suna da mata ba domin cikar jin dadinsu da ikonsu. Kuma da yawan matan na kautar da su bisa ga daidai domin karancin hankali da rashin tunanin sarakunan ko masu ikon. Da yawa wadanda suka mallaki duniya suka hau kan wuyan mutane suna sukuwa, su kuma matan ne ke juya su tamkar rakumi da akala. Mata sau da yawa sun talauta mawadaci, sun kuma kaskantar da mai girma, suka kuma bautar da mai ‘yanci. Ka sani mata sun fitini malamai da masana, sun bata shirin masu tsoron Allah, sun tsiyata ma’azurta, sun mayar da masu ni’ima zuwa marasa ni’ima. Sau da yawa maza na batawa da mahallicinsu har da iyayensu saboda biye wa mace, domin ta rinjayi son su, sun mika mata zuciyarsu. Abin da ba ka sani ba ya kai rarrauna, domin mata ake gina soraye a yi musu kawa ta alfarma. domin su ake sayar da bayi. Saboda a burge su ake cinikin azurfa da lu’ulu’u da zinare da miski da ambar. Haka nan saboda su za ka ga Sarki na hawaye yana umartar askarawansa da su aikata wata aika – aikar. Ni ban yarda ba da ake cewa wai mata su ne a kasa a duniya, ko dai su ne saman na sama.
Game da batun da ake cewa wai mace tamkar namijin saurayi take, wannan ba haka ba ne, amma yadda abin yake a zahiri shi ne irin wannan maza su ne masu koyi da dabi’un mata. Nakan ji mutane suna cewa, “wannan yaron sai ka ce mace.” Amma game da yadda ka kawo dalilanka ta fuskar waka, wannan babu laifi bisa ga rubutu amma cike suke da zuki- ta- malli, musamman ga mutanen da suke neman juya halittar Allah zuwa ga wani abu daban. Wadannan su ne suka yarda da luwadi da fasadi suke aikata barna a cikin addini. Allah madaukakin Sarki ya ambace su a Alkur’ani mai girma kuma ya yi fushi da wannan mummunar dabi’a, inda yake cewa, “yanzu kwa zo wa mazaje a cikin mutane ku ka bar matayenku wadanda Allah Ya halitta domin ku? Babu shakka ku mutane ne masu ketare iyaka.” To wadannan kadai su ne ke danganta maza tamkar mata domin shisshiginsu da barnar su da sabon da ya yi musu katutu a zukata, ba kuma don komi ba sai don bin son zuciya wadda shaidan ke kawata wa musu barna, suna biye masa. Wannan ya sa suka halarta namiji a kan mace domin karkacewar su ga hanya.
Game da zancenka na cewa kyawon saurayi tsiruwar gashin baki da saje da gemu wai yaro na kara kyau da haka da kuma cikar siffa, to wallahi na fada maka ka yi adalci a wannan tafarki, ko da ka fada ba da sakankancewa ba. Domin saje yana sauya kyawon wani saurayi, ko dai ya kara masa ko ya rage masa.
Lallai ka kasa gane cewa jin dadi madaukaki yana nan a wajen mata, a domin haka ma Allah mai girma da daukaka Ya alkawarta wa annabawansa da waliyansa da sauran mutanen kirki mata masu fararen ido a aljanna. Haka kuma Allah ya kaddara cewa babu inda za a samu jin dadi gamamme sai a wajen mata. Da akwai wani abu sabanin haka da an tanade shi a can. Haka kuma Ma’aiki mai tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa, “an sanya min kaunar abu uku a wannan duniya; mata da turare da sanyin ido, yayin sallah. Hakika Allah ya halicci wasu yara samari a aljanna domin su yi hidima ga annabawa da waliyai, domin aljanna gidan hutu ne da jin dadi. Amma su samari babu wani abu gare su da ya wuce wannan hidimar, domin wucewa bisa ga yin haka a ko’ina ne to kayan wuta ne da lalacewa da musiba.
Daga nan ta ce, “ya ku mutanen nan, hakika kun fito da ni daga dakin kunya kun zagaya da ni har na fadi abin da bai kamata a ji ina fada ba. To amma kirazan ‘yantattun mutane na cike da sirrika da abubuwa masu yawa da ke boye a ciki. Kuma duk aiki yana tare da niyyarsa. Ni dai na roki Allah mai girma da Ya yi gafara gare ni, da ku duka da sauran Musulmi baki daya, domin mai yawan gafara ne mai jin kai.” Daga nan ta yi shiru ta daina magana. Muka fita daga gare ta muna masu farin ciki da abin da muka ji daga gare ta, mun kuma amfana, kwarai matuka.
Tsakure Daga Cikin Littafin Alfu Layla.